A karon farko, an ba Bahaushe Kwamishina a Kuros Riba
Shi ne Bahaushe ba farko a tarihi da rike mukamin da ya kai wannan a Jihar
Gwamnan Jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade, ya nada Malam Adamu Uba Musa, Bahaushe na farko a tarihi a matsayin Kwamishina a Jihar.
Aminiya ta gano kuma shi ne dan asalin Arewacin Najeriya na farko a tarihin Jihar da zai taba rike mukamin da ya kai wannan matsayin.
Naxin ya biyo bayan mika sunayen wadanda Gwamnan yake son nadawa Kwamishinoni ga Majalisar Dokokin Jihar domin sahalewarta, inda nan take ta amince.
Kazalika, Majalisar ta kuma amince da nadin Dokta Janet Ekpenyong a matsayin Darakta Janar a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar.
An haifi Adamu Uba Musa ne a garin Ogoja da ke Arewacin Jihar, kuma ya yi karatun firamare da sakandare duk a garin, ya kuma samu Digiri a fannin Harkokin Mulki.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Eteng Jonah Williams, ya shawarci wadanda aka ba mukaman da su zama masu gaskiya da rikon amana.