A karon farko cikin shekara 17, an yi mako 2 ba ruwan sama a Denmark

Rabin da a yi haka tun a watan Janairun 2006

A karon farko cikin shekara 17, an yi mako 2 ba ruwan sama a Denmark

Mamakon ruwan sama

A karon farko cikin shekara 17, kasar Denmark ta shafe sama da mako biyu ba ta ga ko da digon ruwan sama ba, kamar yadda Hukumar Kula da Yanayin Kasar (DMI) ta tabbatar.

Hukumar ta ce, “Akwai alamun da ke nuna shafe tsawon lokaci ba a samu ruwan sama ba na da alaka da sauyin yanayi, amma dai lokaci ne na bincike.”

Galibin kasashen Arewacin Turai dai a ’yan shekarun nan na fama da karancin ruwan sama da kuma karuwar barazanar wutar daji, musamman a Sweden.

Hatta watan Mayun da ya gabata shi ne wanda ya fi kowanne irinsa karancin ruwan sama cikin shekaru 15, kuma ba a hasashen samun ruwan a ’yan kwanaki masu zuwa.

“Idan yau ba a yi ruwa ba, hakan na nufin mun yi kwana 15 ke nan a jere babu ruwan sama, rabon da a samu irin haka tun ranar daya ga watan Janairun 2006,” in ji DMI, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya rawaito

Hukumomin kasar dai sun ce ba lallai ne a samu ruwan saman ba nan da ’yan watanni masu zuwa, lamarin da ake barazanar zai iya haifar da wutar daji.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya