A kasa daliban makarantar Sakandaren Galamawa da ke Jigawa ke karatu
Duk da irin makudan kudin da gwamnatin Jihar Jigawa ke kashewa don inganta ilimi a har yanzu akwai makarantun firamare da kananan sakandare da dalibai ke daukar darasi a kasa ciki har da makarantun da ke hedikwatar jihar.Wakilinmu wanda ya ziyarci makarantar Galamawa a karamar Hukumar Dutse ya ga yadda daliban makarantar sakandare ta Galamawa […]

Duk da irin makudan kudin da gwamnatin Jihar Jigawa ke kashewa don inganta ilimi a har yanzu akwai makarantun firamare da kananan sakandare da dalibai ke daukar darasi a kasa ciki har da makarantun da ke hedikwatar jihar.
Wakilinmu wanda ya ziyarci makarantar Galamawa a karamar Hukumar Dutse ya ga yadda daliban makarantar sakandare ta Galamawa ke karatu a kasa a cikin ajujuwa bakwai daga cikin ajujuwan makarantar.
Ya ce a gaba dayan makarantar bayan kujerun malamai biyar sai kujera 50 da suke wani aji a karamar sakandare galibin daliban suna zama ne a kan kwalaye da katakai.
A wannan makaranta ce dai Shugaban kungiyar Malamai ta Jihar Jigawa Kwamared Ya’u Dutse yake koyarwa.
Kuma lokacin da yake magana ya ce matsalar da aka samu ta rashin kujerun zama ta faru ne daga mai kai wa makarantu kujerun, kuma ba ita kadai ce ke fuskantar haka ba, makarantu da dama suna da makamanciyar irin wannan matsala.
Shugaban Hukumar Ilimi ta Bai-daya (SUBEB) ta Jihar Jigawa, Alhaji Sani Abdullahi Gumel ya tabbatar da samuwar wannan matsala inda ya ce magana ce da ba zai iya budawa ba saboda wanda aka ba aikin kwangilar samar da kujerun yana da wuyar sha’ani, domin idan ya fito ya fadi sunansa zai zama sanadin raba shi da matsayin da yake kai
Gumel ya ce sun samu labarin matsala mai ba da kujerun ya samu amma yanzu an gano maganin matsalar kuma ana nan ana kokarin gyarawa domin samar da kujeru a daukacin makarantun jihar musamman makarantar Gadadin da Galamawa da Kaci da makarantar ’yan mata ta baure ta da ke kusa da Marabusawa Garu.