A kasashen da suka ci gaba ba a ba mutum shugabanci sai ya yi aikin tallafa wa jama’a – dankwambo

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibarhim Hassan dankwambo, ya ce a wasu kasashen duniya da suka ci gaba ba a ba mutum shugabanci sai ya gudanar da wasu ayyuka na tallafa wa jama’a kamar yadda kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah take yi wadda zai yi wuya ta ba mutumin da bai san hakkin jama’a ba shugabanci.Gwamna dankwambo […]

A kasashen da suka ci gaba ba a ba mutum shugabanci sai ya yi aikin tallafa wa jama’a – dankwambo
A kasashen da suka ci gaba ba a ba mutum shugabanci sai ya yi aikin tallafa wa jama’a – dankwambo

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibarhim Hassan dankwambo, ya ce a wasu kasashen duniya da suka ci gaba ba a ba mutum shugabanci sai ya gudanar da wasu ayyuka na tallafa wa jama’a kamar yadda kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah take yi wadda zai yi wuya ta ba mutumin da bai san hakkin jama’a ba shugabanci.
Gwamna dankwambo ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wurin atisayen da kungiyar ta shirya ga ’yan agajinta a Sansanin Alhazai na Jihar Gombe a makon jiya inda ya yaba wa kungiyar bisa kokarin da take yi wajen tarbiyyantar da matasa.
Ya ce irin wannan aiki na horar da matasa ba a koyar da shi a makarantu, dole sai a fili kuma atisaye ne na musamman da ake koya yadda za a kula da marasa lafiya a inda hadari ya faru ko a wurin taro da yadda za a kula da matafiyi da yadda za aa kula da wanda ya bata sauransu.
Gwamna dankwambo, ya ce ya yi matukar farin cikin ganin irin wannan aiki da kungiyar Izala take yi, inda ya ce yanzu an shigo shekarar da ’yan siyasa za su yi ribibin amfani da matasa marasa tarbiyya suna ba su kwayoyi da makamai da ’yan kudi don tada husuma saboda biyan bukatun kansu. “Don haka ina kira ku kara kwazo wajen ceto matasa domin dukkankun shaidu ne na abin da ya faru a baya na rikicin zaben 2011 kuma a yi addu’a kada Allah Ya sake nuna mana irin wannan al’amari,” inji Gwamnan.
Sai Gwamnan ya mika kyautar motoci uku kirar Toyota HILUd ga kungiyar don ba su damar gudanar da ayyukansu cikin sauki.
Shugaban kungiyar Izalar na Jihar Gombe Alhaji Salisu Muhammad Gombe, ya bayyana Gwamna dankwambo a matsayin shugaba adali mai kishin al’ummarsa, kuma ya yi masa godiya ta musamman bisa daukar nauyin gudanar da taron na ’yan agaji.
Alhaji Salisu Gombe, ya ce kungiyar Izala ta Jihar Gombe a shirye take wajen hada hannu da gwamnatin jihar don bunkasa tarbiyyar matasa da inganta harkar ilimi.
Ya tabbatar wa Gwamnan cewa kungiyar za ta yi amfani da motocin wajen shiga lungu da sakon jihar don yada manufofin addinin Musulunci da wa’azi musammam ga wadanda suke yankunan karkara.