A kawar da bambancin addini da kabilanci a Arewa – Reuben Kwasu
Malam Adamu Rubean Kwasu, Shugaban kungiyar dalibai “FTC” . makarantar horar da maaikata da ke Kalaba, Jihar Kuros Riba, ne ya bukaci a kawar da bambancin addini da na kabila, don ci gaban Arewa, musamman in an yi la’akari da ayyukan magabatan baya.A jawabin da ya yi ranar dalibai da aka yi wa lakabi da […]
Malam Adamu Rubean Kwasu, Shugaban kungiyar dalibai “FTC” . makarantar horar da maaikata da ke Kalaba, Jihar Kuros Riba, ne ya bukaci a kawar da bambancin addini da na kabila, don ci gaban Arewa, musamman in an yi la’akari da ayyukan magabatan baya.
A jawabin da ya yi ranar dalibai da aka yi wa lakabi da “ranar Arewa,” ya yi nuni da cewa matukar ana son yankin ya dawo da martabarsa, sai shugabanni da wadanda suke da alhakin kula da tarbiyya da gina yankin kowa ya watsar da son abin duniya ya rungumi yankin ka’in-da na’in.
“Tilas sai an sanya kishi tare da kawar da duk wani bambancin kabila ko na addini, da kuma taimakon marasa galihu an hada kai tare da yin koyi da yadda manyan arewa da suka gabata irin su marigayi Sa Amadu Bello Sardauna da Sa Abubakar Tafawa Balewa da irin su Mudi Spikin, Malam Aminu kano suka yi wajen hada kan al’umma da raya yankin Arewa ne kadai zai kawo wa Arewa, ci gaba da zaman lafiya, musamman ma irin yadda wasu yankunan kasar nan suke kallon yankin mu tamfar wanda ya fi kowanne talauci da kuma almajiranci. Hakki ne wanda ya rataya wuyan kowannen mu da muy i abin da zai kawo mana mafita daga halin da yankin mai dimbin daraja da kuma tarihi ya kuma haifar da mashahuran mutane”.” inji shi.
Rubean Kwasu ya ci gaba da cewa “ yau sakaci da rashin hadin kai irin namu da kyamar juna ya haifar mana da matsaloli , har ta kai ga a duk inda dan Arewa yake yana cikin zullumi da tunanin halin da yankin ya shiga, musamman tabarbarewar tsaro, lamarin da manyan da na ambata suka gabata ba haka suka zauna da juna ba, sun rungumi kowa ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba”. Har wa yau ya nuna takaicinsa, kan irin yadda wasu gungun mutane marasa kishi suka yi watsa-watsa da wani sashe na Arewacin kasar nan, domin cimma burin kashin kansu.
Shi kuwa Malam Adamu Yusuf babban bako mai jawabi, kira ya yi da a koma halin dattako da shugabannin mu na Arewa irin su Sa Kashim Ibrahim da danmasanin kano, Maitama Sule suke nunawa duk wani dan Arewa suke kira da a ci gaba da zama kan haka. “Mu kuma mu kawar da duk wasu bambance-bambance da ke tsakanin mu yayin da aka yi maganar Arewa babu sauran nuna ni kabila kaza ne, sauran nuna wani son zuciya, mu kawar da shi, to idan aka yi haka Arewar mu za ta dawo kamar yadda take ba za mu samu matsala ba”.inji shi
A karshe ya bayyana babban kalubalen da suke fuskanta, shi ne na rashin samun mahallin makarantar na dindindin, don haka ya nemi gwamnatin tarayya ta duba matsalar tun da ko da yaushe ana samun karuwar dalibai daga sassan kasar nan da suke zuwa karatu.