A kawar da bambancin siyasa don tunkarar yaki da rashawa – Tsanni

Daraktan kungiyar Gyaran Najeriya ta TNFI, Alhaji Abubakar Tsanni ya ce matakan da gwamnatin  Jam’iyyar APC ke xauka don kawar da cin hanci da rashawa da rashin tsaro, ya samu karbuwa a kasar nan ne saboda waxanda ba su bata sunansu ba, sun tunkari yaki da munanan xabi’un da suka illata kasar, suka dakile ci […]

A kawar da bambancin siyasa don tunkarar yaki da rashawa – Tsanni
A kawar da bambancin siyasa don tunkarar yaki da rashawa – Tsanni

Daraktan kungiyar Gyaran Najeriya ta TNFI, Alhaji Abubakar Tsanni ya ce matakan da gwamnatin  Jam’iyyar APC ke xauka don kawar da cin hanci da rashawa da rashin tsaro, ya samu karbuwa a kasar nan ne saboda waxanda ba su bata sunansu ba, sun tunkari yaki da munanan xabi’un da suka illata kasar, suka dakile ci gabanta tsawon shekaru suka hana Najeriya kaiwa ga matsayinta a tsakanin kasashen duniya.
Daraktan ya bayyana haka ne a wani taron ’yan jarida da ya kira a Abuja game da al’amuran da ke wakana a siyasar Najeriya, ya ce yaki da almundahana wata dama ce da Najeriya ta samu da ya dace a yi amfani da ita wajen bunkasa ci gaban kasa.
Ya bukacii masu sukar yaki da cin hanci da rashawa, su yi watsi da bambancin siyasa su tallafa wa Shugaban kasa. “Duk wanda ya sanya Najeriya a cikin tunaninsa, zai fahimci cewa an samu sauyi a xaukacin shirin bunkasa tattalin arzikin kasa. Idan aka yi la’akari da yadda kasar nan ta kasance, sai a tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Buhari na bisa turba tagari. Domin xaukacin ’yan Najeriya sun san cewa an samu ingantar wutar lantarki da tsaro da man fetur. Sannan zamanin keta doka ko yi mata karan-tsaye ya wuce,” inji shi.
Shugaban kungiyar ta TNFI ya nuna gamsuwa game da wannan yakin da ake yi da cin hanci da rashawa, inda ya ce yana da tabbaci yaki da cin hanci da rashawa da Shugaban kasa zai haifar da xa mai ido, don haka ya roki ’yan Najeriyasu bayar da goyon baya ga Shugaban kasar don cimma burinsa na buxe sabon babin inganta rayuwar al’umma ta yadda za su rika tutiya da kasarsu.
Abubakar Tsanni ya bayyana niyyar kungiyarsa ta yin aiki kafaxa da kafaxa da gwamnati don cusa akidar kishin kasa a zukatan ’yan Najeriya, ta yadda za su bayar da goyon baya da gudunmawa wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ta samu nasara wajen yaki da ta’addanci, inda ya yaba wa hafsoshin soja da suka nuna kishin kasa a jagorancin sojin da suke yaki da ’yan Boko Haram.
Dangane da masu fafutikar kafa kasar Biyafara, ya ce alkiblar kungiyarsa, shi ne taimaka wa gwamnati wajen shawo kan masu nufin yi mata tarnaki. Kuma ya ce za su cimma wannan manufa ta su ne ba tare da sun yi taho mu gama da al’umma ba.
Ya ce, mafi yawan matsalolin da ke fuskantar Najeriya da suka shafi cin hanci da rashawa da tsaro, an samu gagarumar nasara a kansu.