‘A kebe 13 ga Fabrairu don tunawa da Janar Murtala’

Shugaban kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Kano, Malam Balarabe Babale Gajida ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kebe 13 ga Fabrairun kowace shekara a matsayin Ranar Tunawa da marigayi Shugaban kasa Janar Murtala Ramat Mohammed tare da bullo da hanyoyin tunawa da tsohon shugaban domin a cusa wa matasa da jama’a kishin kasa ta hanyar koyi […]

‘A kebe 13 ga Fabrairu don tunawa da Janar Murtala’
‘A kebe 13 ga Fabrairu don tunawa da Janar Murtala’

Shugaban kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Kano, Malam Balarabe Babale Gajida ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kebe 13 ga Fabrairun kowace shekara a matsayin Ranar Tunawa da marigayi Shugaban kasa Janar Murtala Ramat Mohammed tare da bullo da hanyoyin tunawa da tsohon shugaban domin a cusa wa matasa da jama’a kishin kasa ta hanyar koyi da kyawawan halayen marigayin.
Malam Gajida ya yi wannan kiran ne a yayin taron laccar tunawa da marigayi Janar Murtala da Muryar Talaka da hadin gwiwar Rudunar Adalci ta Najeriya suka shirya a Babban dakin Karatu na Murtala da ke Kano.
Ya ce “akwai bukatar a sanya ranar 13 ga watan Fabrairun kowace shekara ta kasance ranar hutu a Najeriya, sannan ya kamata a sanya tarihin rayuwar marigayin a manhajar ilimi ta kasa don cusa kishin kasa a zukatan dalibai.”
Shugaban ya ce abin takaici ne yadda a yau hukumomin kasar nan suka juya baya tare da mantawa da tarihin Janar Murtala wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen dinke kasar nan da yaki da almundahana.
A jawabin Dokta Mahmuda Lawan na Jami’ar Bayero ta Kano, ya bayyana marigayi Janar Murtala da jarumin shugaba kuma jajirtacce, wanda yake tunkarar duk al’amuran mulkin kasa da himma da jarumtaka.
Dokta Lawan ya nuna takaicinsa kan tabarbarewar al’amura a Najeriya tare da rashin kishin kasa da almubazzaranci da dukiyar jama’a da mahukunta ke yi a yanzu, inda ya bukaci daukacin ’yan Najeriya su yi koyi da managartan halayen shugabannin da suka gabata, maimakon mayar da hankali wajen tara dukiya da hadama.
A jawabinsa, shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, Alhaji Abdulkarimu dayyabu, ya soki shirin taron kasa da ake shirin gudanarwa. Ya ce maimakon taron kasar, kamata ya yi a gudanar da taron kwato dukiyar kasa da aka sace.