A kokarin rage kiba ta hadiye roba mai tsawon santimita 30
Wata budurwa mai suna Diao Lu mai shekara 22 da ke birnin Guangzho a kasar China ta hadiye roba don ta taimaka mata wajen yin amai, inda yanzu haka ta janyo mata rashin lafiya. Wannan abu da ta aikata ya sa ta zama mace ta farko da ta taba hadiye abin da zai iya taimaka […]
Wata budurwa mai suna Diao Lu mai shekara 22 da ke birnin Guangzho a kasar China ta hadiye roba don ta taimaka mata wajen yin amai, inda yanzu haka ta janyo mata rashin lafiya. Wannan abu da ta aikata ya sa ta zama mace ta farko da ta taba hadiye abin da zai iya taimaka mata wajen mayar da abinci a dalilin rage mata kiba.
Rahotanni sun ce, Diao Lu, ta je asibitin garin a ranar 3 ga Disamban bana, ta bayyana wa likita cewa ta yi kuskuren hadiye robar zukar abin sha, kuma robar ta shige har cikin makogwaronta, hakan ya sa likitan asibitin ya yi amfani da na’urar daukar hoton cikin marar lafiya, inda ya gano robar da ta hadiye ta kai fadin santimita 1.9 da tsawon santimita 30. Bayan gwajin, likitan ya gano robar da kauri da tsawo hakan ya sa ya fara tambayarta kan abin da ya faru.
Bayan tambayoyin ne ya gano cewa akwai rashin gaskiya game da bayanan marar lafiyar, daga bisani Diao ta gane cewa karya da ta yi ba ta da amfani, sai ta bayyana wa likitan cewa, ta sayi robar ce a kasuwar Intanet don taimaka mata wajen rage kiba, kuma tana saka robar ce a cikin makogwaronta bayan ta ci abinci don hakan zai taimaka mata wajen duk wani abinci da ta ci ba zai narke ya yi mata amfani ba, amma sai wata rana ta yi kuskuren hadiye robar gaba daya.
Hoton D-ray da aka yi ya nuna tun daga farkon robar har zuwa karshenta duk ta shige a cikinta, wani bangaren robar yana kusa da karshen makogwaronta. Likitan ya yi nasarar ciro robar, kuma lokacin yi mata tiyata an gano tana dauke cutar gyambon ciki.
Mataimakin Shugaban Likitocin da ke sashin agajin gaggawa na Beijing, Zhang Hanyu, ya ce, yanzu haka ana ci gaba da samun matsala a tsakanin ’yan matan China da suke amfani da irin wannan roba wajen rage kiba, musamman masu matsalar kafafu wajen tafiya saboda kibar da suke da ita.
Likintan ya ce, wannan shi ne karo na farko da aka samu wadda ta yi kuskuren hadiye robar.