A kokarin tserewa, mai garkuwa da mutane ya yanke jiki ya fadi ya mutu
An kuma kama ragowar masu garkuwar su takwas
Wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne domin karbar kudin fansa ya yanke jiki ya fadi sannan ya mutu nan take a kokarinsa na tsere wa sojoji a Jihar Bauchi.
Lamarin ya faru ne lokacin da mutumin yake kokarin guje wa wani shingen bincike na sojojin bataliya ta 133 ta musamman da ke Azare a Jihar.
- Dan ‘jam’iyyar adawa’ ya zama Shugaban Majalisar Dokokin Imo
- Sama da mutum 100 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Kwara
Kazalika, sojojin sun kuma kama wasu mutum shida da su ma ake zargin masu garkuwar ne kuma tuni an mika su a hannun ’yan sanda.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Ahmed Wakil ne ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa a ranar Talata a Bauchi, inda ya ce tuni suka fara fadada bincike a kan lamarin.
Ya ce bincikensu na farko-farko ya gano cewa wadanda ake zargin sun sace wata daliabr Jami’ar Jihar Bauchi ce da ke Gadau, wacce take zaune a unguwar Federal Low Cost a garin na Azare, tare da motarta kirar Toyota Camry.
Wakil ya ce jim kadan da samun rahoton hakan ne sojojin da ke aiki a shingen suka tare sannan suka kwace motar ta sata, sannan suka ceto wacce aka sace ba tare da ko kwarzane ba.
Kakakin ’yan sandan ya kuma ce daga cikin kayayyakin da suka kwata a hannun masu garkuwar har da wukake da guraye da wayoyin salula guda takwas.