A koya wa yara yadda za su rike kansu a gaba – Hajara S. Abubkar

Hajiya Hajara Sani Abubakar ita ce Shugabar Otal din Zaranda da ke a Bauchi, tsohuwar malama a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya da ke Bauchi, ta bayyana wa Aminiya tarihinta da yadda take gudanar da gidauniyarta da sauran kalubalen rayuwa: Tarihina Da farko  a firamaren Kwalejin Horon Malamai ta Bauchi (BTC) na fara karatu […]

A koya wa yara yadda za su rike kansu a gaba – Hajara S. Abubkar

Hajiya Hajara Sani Abubakar

Hajiya Hajara Sani Abubakar ita ce Shugabar Otal din Zaranda da ke a Bauchi, tsohuwar malama a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya da ke Bauchi, ta bayyana wa Aminiya tarihinta da yadda take gudanar da gidauniyarta da sauran kalubalen rayuwa:

Tarihina

Da farko  a firamaren Kwalejin Horon Malamai ta Bauchi (BTC) na fara karatu saboda a nan mahaifina yake aiki daga baya da aka maida shi Maiduguri lokacin Jihar Bauchi tana Arewa maso Gabas sai na ci gaba da karatu a can kuma bayan ya yi ritaya ya koma Kano sai na je Sakandaren ’Yan mata (GSS) ta Kura a Jihar Kano. Bayan na kammala sai na wuce Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Jihar Bauchi (BACAS) a Bauchi. Saboda mahaifina dan Jihar Bauchi ne yana da kishin jiharsa, shi ya sa na dawo na ci gaba da karatu a Bauchi. Duk ’ya’yansa idan suka kare sakandare a Kano akan dawo da su Bauchi ne su ci gaba da karatu. Bayan haka sai na shiga Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere  ta Tarayya (Federal Polytechnic) da ke Bauchi, na karanta aikin otal da girke-girken abinci. Da na gama sai na je aiki yi wa kasa hidima a Jihar Kwara daga baya na dawo Bauchi  hidimar kasar na yi aiki a otal din Zaranda. A lokacin Malam Ahmed ne shugaban  otal din Zaranda da na kammala sai ya ba ni aiki. Na shafe shekara 15 ina aiki da su, duk wasu mukamai na wurin ba wanda ban rike ba har na kare na zama shugabar hotal din. Da aka yi canjin gwamnati , sai aka cire masu kula da otal din Arewa daga kula da otal din, aka kawo masu kula da otal na Nanet da  suka dawo sai na fita domin an ce ko in yi aiki da Nanet ko in dawo Arewa Hotels.

Da farko Arewa ne suka dauke ni amma daga baya sai na je na bude wani wajen cin abinci, ina cikin tafiyar da wannan wuri ne kuma aka zo aka nemi in koyar a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya da ke Bauchi kan abin da na karanta. Bayan na yi shekara bakwai ina koyarwa sai Jihar Bauchi a karkashin Ma’aikatar Kasuwanci ta sake dauka ta aiki aka ba ni kula da otal din  Zaranda. Saboda akwai matsalolin rashin shugabanci tunda yawancin masu aiki a wurin ba ma’aikatan da suka dace ba ne. To saboda wannan matsala ce aka ce in zo in taimaka in dawo da martabarsa kamar yadda yake a baya, shi ne tun shekara biyu da suka wuce nake ta fafatawa har zuwa yanzu.

Me ya ba ki sha’awar karanta aikin otel?

Abin da ya ba ni sha’awa shi ne akwai baffana Alhaji Usman Salisu yana da abokinsa lokacin ina makarantar sakandare idan na yi hutu yakan zo ya dauke ni in je hutu a gidansa, to shi ma akwai abokinsa wanda matarsa ma’aikaciyar otel ce, kowane lokaci idan muka je gidan idan za a yi buda baki sukan gayyace mu sai mu je daga Zariya zuwa Funtuwa, idan muka je a cikin sa’o’i kadan takan hada abin buda baki da nakan ji mamaki. Tun a lokacin ina karama kuma sai aka fada mini cewa abin da ta karanta ke nan, tun daga lokacin na kudiri niyyar cewa idan na samu dama zan karanta aikin yadda ake hada cimaka wato catering amma ba otal ba. Domin asalin abin da nake so in karanta shari’a ce. A lokacin Sarkin Hardawa Allah Ya jikansa abokin Babanmu ne kuma yana Kwamishina a Ma’aikatar Kasuwanci da muka gama makaranta ni da ’yarsa da sauran ’yan uwa mu hudu ya sa aka ba mu gurbin karatu a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Tarayya da ke Bauchi ya ce mu je mu karanta aikin otal da yadda ake dafa abinci. Lokacin ana gina otal din Zaranda ya ce mana idan aka gama ku za ku zo ku yi aiki a nan wurin insha Allah, kuma sai da wannan abin ya tabbata tun yana da rai ya gani.

Wadanne matsaloli kike fuskanta a otal din a yanzu?

Matsalolin ba daga wannan gwamnati ba ce daga gwamnatin da ta shude ce yawancin matsalolin suka taso amma ga dukkan alamu muna ganin nasara, tunda muka kai kukanmu wajen Gwamna mun samu kyakykyawar fahimta. Har ma ya sa ’yan ta’adda da suke shigo mana su ki fita an fitar mana da su biyu. A yanzu otal dinmu mutane masu mutunci suna zuwa suna kwana, amma da saboda ganin ’yan bangar siyasa ne suke zuwa ake ba su takardu daga waccan gwamnatin mutane da yawa suna tsoron shigowa. Idan muka dubi bangaren ma’aikatanmu akwai matsala kuma da wasu matsaloli na ainihin shi otel din saboda otel din ya dade shekara 35 yana neman a tallafa masa a gyara, su ma ma’aikata a taimake su kudadenmu da muke bi a wancan gwamnati Gwamna ya taimake mu kamar yadda yake taimaka wa ’yan fansho. Da na ji yana taimaka wa ’yan fansho ina jin dadi saboda na san wata rana mu ma zai dawo kanmu ya samu ya biya mu kudadenmu koda a hankali ne, mu samu mu biya bukatunmu, mu biya ma’aikatanmu mu tallafa musu. Kuma babbar matsalarmu ita ce maganar ma’aikata a samu a biya su, suna da iyalai kowa yana so a ce iyalinsa idan ya fito da safe ya bar musu abin da za su ci, shi ma zai fi jin dadi ya yi aiki idan babu wannan ko ya zo wajen aiki sai dai kawai a yi hakuri da shi. Akwai matsaloli da yawa da suke tasowa amma saboda abubuwan da suke kan (Gwamna) dole mu daga masa kafa.

Wane sako kike da shi ga ma’aikatanku

Sakon da nake da shi shi ne su kara hakuri. Ina matukar jin tausayinsu saboda duk mai iyali ya san yadda abubuwa suke saboda akwai rashin lafiya akwai ciyarwa, dole ne ka ba yaro abinci ba yadda za a yi a ce ka ajiye yaro ka bar shi a cikin yunwa. Ko matarka ka bar ta cikin damuwa kullum tana yaya za ta yi. Ina matukar jinjina musu da wannan hakuri da suka yi don sun riga sun yi hakuri kuma Allah Ya kara musu hakuri.

Bangaren kasuwanci da yanayin yadda tattalin arziki yake ga yanayin matsi da jama’a suke ciki yana shafar harkokinmu, saboda a da ka ga mukan samu kasuwanci, mutane suna zuwa daga Abuja da Legas.

Wadansu kan ce abin da ya sa ba sa zuwa otel din gwamnati su kwana shi ne an sa kudi da yawa, wane bayani kike da shi ga masu sauka a nan?

Muna da kyakkyawar fahimta tsakaninmu da mutane amma idan ka ga yadda  Zaranda yake da kyau, sai ka dauka dakunanmu suna da tsada. To amma dakunanmu ba su da tsada, karamin dakinmu Naira dubu 10ne, amma idan ka zagaya ka shiga kananan otal za ka samu dakunan ba su kai namu kyau da komai ba amma kudinsu ya fi namu. Kuma a kowane lokaci idan mutane suka zo muna da tabbacin cewa za mu rage musu. Misali idan ka zo ranar Juma’a zuwa Lahadi akwai abin da muke ragewa.

Bayan aikin ofis ko akwai wani abu da kike yi a gida na taimakon yara ko marayu ko matasa? 

Ina da gidauniya mai suna Zam-Zam kuma ina cikin kungiyoyin mata saboda a irin wurin da nake zaune mata da nake zaune da su suna cikin damuwa. Kuma inda na yi aure surukata ita mai tausayi ce kuma tana ganin ’ya’yanta suna da halin da za su iya ajiye mata abinci, ba don ta dafa ba takan bai wa makwabta abinci da safe, mutane sukan shigo su zo da kwanukansu, ta ba su shinkafa da masara da hatsi.  Shi ya sa na kirkiri wannan kungiya ta matan Wunti

wanda idan na samo wasu abubuwa ta wannan kungiyar nake raba wa mata, akwai lokacin da aka taba ba ni wani matsayi a Abuja a cibiyar mata wato Women Centre aka ba mu kayayyakin da aka kawo daga kasashen waje irin su keken dinki da sauran kayayyaki na zo na rarraba wa mata.

Wane aiki wannan gidauniya take yi?

Gidauniyar tana samar da abinci ga marayu kuma akwai yara da za ka samu ba marayu ba ne amma marayu sun fi su gata, irin wadannan yara nakan ba su kudin makaranta. kuma sukan zo da matsalolin kudin makaranta da takalma da abinci, to ina iya kokarina in samu kayan abinci a wajen mutane da ni kaina in rarraba musu. Haka kuma mutanen da ban sansu ba sukan zo su same ni don in taimaka musu da wadannan abubuwa.

Wani abinci kika fi sha’awa?

Abincin da na fi sha’awa ba wani abincin a zo a gani ba ne, nakan yi kokari in ci duk wani abin da nake so da kuma wanda ba su kai komai ba, ko da abinci nasa a gaba wata rana idan na tuna wadansu suna neman irin wannan abinci su ci amma ba su da shi nakan yi kokari in ci. Shi ya sa wajen aikina komai za a rasa amma kada a yarda a hana ma’aikatana abinci kuma duk abin da aka dafa musu zan iya cinsa.

A jerin abincin da kuke da su a nan wanne ya fi ba ki sha’awa ?

Abincin da ya fi ba ni sha’awa shi ne tuwon shinkafa da miyar kuka.

Yanzu yayanki nawa?

’Ya’yana biyar ne.

Ko akwai wanda suke so su yi irin aikinki?

Akwai wanda suke son yin abin da nake yi, amma kowa yana da irin nasa bangaren amma ’ya’yana wanda na aurar da su gaskiya mazansu na yaba girkinsu, saboda na koya musu girki da iya tsabtace gida da kayan dakin miji saboda haka ko yanzu ina farin ciki.

Wane tufafi kika fi so ?

Na fi sha’awar doguwar riga da hijabi musamman idan ina ofis.

Yaya kike hutu?

Lokacin da na fi daukar hutuna a shekara shi ne lokacin aikin Hajji in tafi Saudiyya, can ma ba hutu nake zuwa ba amma dai na bar inda nake don yawancin madafa abincin mahajjata ni nake kula da su lokacin Gwamna Ahmad Mu’azu da lokacin Malam Isa Yuguda.

Gwamnati ta fara yi wa alhazai abincin gargajiya ko an nemi shawararki, ko kuma kina da wata shawara da za ki ba su?

Wannan gwamnati ba ta nemi shawarata ba kuma ba ta ce in ba su ma’aikata ko in je in yi musu aiki ba, amma insha Allahu idan muna cikin rayayyu badi zan nemi haka, saboda ba sai ka jira an kira ka a kan abin da ka sani ba, kai ma za ka iya zuwa da kanka tunda kai ka san me mahajjata suke so.

Wace shawara za ki ba mata da matasa?

Shawarar da zan ba mata ita ce su horar da ’ya’yansu lokacin da suka fara wayo, musamman mace ya zamo za ta iya rike kanta da gidan mijinta, saboda idan ka koya wa ’ya mace sana’a ko yadda za ta zauna a gidan mijinta, to wannan mijin ba zai sa mu matsala ba. Sai dai sam barka, su ma maza ba a bar su a baya ba, ya kamata a horar da su sanin mutunci da girmama na gaba saboda su zama mutanen kirki su taimaka wa al’umma.

A karshe ina kara gode wa maigidana saboda ya taimake ni kwarai da gaske a rayuwata duk abin da na ce zan yi idan mai kyau ne ya ma fi ni so in yi wannan abu.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos