A-Kurkura: Guba ko Magani?
Wani malamin makarantar matan aure, ya bayyana cea yadda matan aure ke ta’ammali da A-Kurkura ya wuce yadda al’umma ke tunani
A-kuskura ko kuskura, kamar yadda ake kiran sa a wasu wurare da dama, wani sanannen ruwan sinadari ne mai kama da maganin gargajiya da ake amfani da shi ta hanyar kurkurawa a baki. Sinadarin a-kuskura yana da launin kasa-kasa tare da wani dandano mai hamami da kanwa-kanwa yayin da aka zuba shi a baki.
Dakta Abba Sagir, malami a Sashen Harsunan Nijeriya da ke Jami’ar Jihar Nasarawa, Keffi, ya shaida wa wakilinmu cewa sunan a-kuskura ko kuskure ya samo asali ne daga kalmar Hausa ta “kurkurawa”, wacce ke nufin guntsar ruwa a baki, ana kurkurawa da nufin tsabtace baki, musamman yayin alwala ko bayan cin abinci.
“Ina ganin cewa masu amfani da sinadarin a-kurkura ko kuskure sukan guntse shi a bakinsu na tsawon ’yan mintuna suna kurkurawa, sai aka ba shi suna kuskure ko kuma a-kuskura,” in ji shi.
Bincike ya nuna kasa da minti daya da fara kuskura sinadarin a cikin baki, zai fara ba da caji ta hanyar bin jinin jiki tare da haifar da jiri da nauyin jiki, wanda ke fara tasiri daga tsakiyar kai har zuwa yatsun kafar wanda ya kuskura.
- Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa
- ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa
- Alhazan Jigawa sun angwance bayan kammala aikin Hajjin bana
Haka kuma, a cikin wannan dan karamin lokaci dai, cikin wanda ya kuskura kan kada, musamman idan sabon shiga ne. Wannan ne ke haifar da amai, ganin jiri, samun maye ko tangadi a hanya, ko kuma yin gudawa.
Sai dai bincike ya nuna cewa cajin da kuskure ke bayarwa bai fiye dadewa sosai ba. Cajin da ake samu nan take yana fara sauka sannu a hankali cikin kankanen lokaci. Duk da haka, masu amfani da shi da dama da aka zanta da su sun yi ikirarin cewa bayan cajin kuskure ya sauka, yana magance masu cututtukan basir, kasala, sanyi, ciwon ido, da kuma kara karfin jima’i.
‘Dalilin da muke amfani da shi’
Musa kanin Mai Dawa, mai shekara 35 kuma bakaniki a Zariya, ya amince cewa ya kamu da amfani da kuskure. Ya ce yana amfani da shi sau bakwai a rana, domin yana ba shi kuzari da karfin aiki.
“Na riga na kamu da shi, ba zan iya dainawa ba. A duk lokacin da na kurkure baki da shi sai in ji kamar ina saman duniya, yana sa ni jin karfi da kuzari wajen gudanar da aikina,” in ji shi.
Ya kara da cewa yawancin matasan da ke aiki a garejinsu suna amfani da kuskure ba don magani ba, sai don samun nishadi da kuzarin aiki.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa ana sayar da kuskure a kananan kantunan magunguna, musamman wadanda ba su da rajista, kuma mutum na iya sayen sa da kudi kadan kamar Naira 200 kacal.
Amina Sanda, wata bazawara mai ’ya’ya hudu daga Unguwar Dankal dan Magaji a Zariya, ta ce tana amfani da kuskure domin samun kuzari wajen kasuwancin kulikuli da take yi, da kuma samun sauki daga abin da take dangantawa da matsalar aljanu.
Haka kuma, Adamu Garken Haka, mai mata uku da ’ya’ya 24, ya ce yana amfani da kuskure a matsayin abin kara karfin jima’i, kuma yana ganin yana taimaka masa wajen magance mura da gajiyar jiki.
‘Ina sayar da kwalabe 500 a rana’
Aminiya ta tattauna da wasu daga cikin dillalan da suke sana’ar sayar da kuskure a Zariya, wadanda suka nemi a sakaya sunayensu da kuma inda suke gudanar da sana’arsu.
daya daga cikinsu ya bayyana cewa asalin maganin ana kawo musu da shi ne daga kasar Ghana da kuma Kudancin kasar nan. Ya kara da cewa an yi shi ne domin magance ciwon kai da mura, tare da kariya daga aljanu da mugayen ruhanai.
Ya ce akwai nau’o’i takwas na kuskure, kuma biyu daga cikinsu sun fi shahara saboda saurin tasirinsu.
A cewarsa, dillalai da masu sayar da kuskure suna samun riba mai yawa saboda yawan masu amfani da shi.
Wani mai sayarwa a Unguwar dan Magaji ya ce yana sayar da sama da kwalabe 500 a rana, kuma maza da mata na amfani da shi sosai.

Matan aure ne kan gaba a Zariya
Rahotanni da bayanai da Aminiya ta tattaro sun nuna cewa ana ta’ammali da wannan magani fiye da kima har ya zama madadin wasu abubuwan maye da aka haramta.
Malaman addinin Kirista da Musulunci da aka tattauna da su sun jaddada cewa addinan biyu ba su amince da amfani da duk wani abu mai sa maye ba.
Daya daga cikin limaman Juma’a, wanda har hudubar Juma’a ya yi a kan yadda matan aure suke ta’ammali da Kuskure, mai suna Al’kali Dikko Isiyaka Ibrahim, ya yi wa Aminiya bayanin dalilin da ya sa ya shirya hudubar ta musamman a kan yadda amfani da Kuskure ya zama ruwan dare a cikin al’umma.
Imam Dikko ya ce, saboda shi malamin makarantar Islamiyya ne da yake karantar da matan aure, shi ya sa ya san yadda matan aure ke ta’ammali da A-Kurkura fiye da sanin al’umma.
Al’kali Dikko ya yi kira da magidanta da su kula, su kuma sa ido sosai a kan iyalansu, domin abin ya yi yawa.
Imam ya ce, duk wani abin da za a yi amfani da shi ya sa maye, ko da halas ne a mahangar Shari’a Musulunci, amma har idan an sha zai sa a yi maye, to amfani da shi ya haramta.
Fasto Dan Ayuba, daya ne daga cikin manyan masu kula da Cocin Katolikan da ke Wusasa Zariya, ya ce: “Addini bai yadda da yin amfani da duk wani abu da ke sa maye ba. Kuma abin, ko da za a ce idan kana da ciwo idan ka yi amfani da shi za ka warke, to ba a yarda ka yi amfani da shi ba a matsayin magani.”
A-Kurkura ya zama ruwan-dare a Bauchi
Jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin da wannan hali na amfani da a-kuskura ke kara yawaita a tsakanin matasa maza da mata.
Wata mata mai suna Rabi Muhammad da ke garin Bauchi ta ce yayanta ne ya kawo mata kuskure a matsayin magani. Ta ce wata rana ta taba a jiye shi a gida, danta yaro karami ya dauka ya kuskura, kuma nan take ya fadi, ya fita daga hayyacinsa, idanuwansa suka rufe, da kyar aka samu ya farfado.
Binciken da wakilinmu ya yi ya gano cewa wannan sabon salon shaye-shaye mutane na yin sa a fili ko a wuraren zaman hutawa da shakatawa.
Haka kuma masu sayar da taba sigari, masu sayar da magungunan gargajiya da masu kayan tireda a mafiya yawansu sukan sayar da shi.
A Bauchi an samu ra’ayoyi mabambanta kan dalilan da suka sa matasa ke amfani da shi.
Wasu sun ce magani ne da ke kashe musu duk wata cuta da ke cikin bakinsu in sun kuskura. Wasu kuwa sun ce sinadarin yana sanya su yin barci mai dadi, kuma idan sun farka sai su ji su wasai ba tare da gajiyar jiki ba.
Wani matashi mai suna Awwalu Barde ya ce ya koyi kuskurawa daga wani shugaban matasa da yakan ba su duk lokacin da za su je taron siyasa ko wasu tarurruka. Ya ce idan suka kuskura za su ji abin ya bi jikinsu, ya mike masu gabobi ba kasala, kuma za su dade a wartsake ba tare da gajiya ba.
Wata mace mai suna Hajiya Murja dantani ta shaida wa wakilinmu cewa masoyinta ne ya koya mata shan a-kuskura a matsayin maganin gajiya, inda sukan sha su yi barci su nishadantu.
Sai dai dukkan matasan sun ce a-kuskura ba shi da wata illa, illa wartsakarwa da cire gajiya a jiki.
Wani Malamin addinin Musulunci mai suna Sayyadi Ibrahim Imam Isma’il ya ce duk abu in har yana shafar kwakwalwa, yana kawar da hankali, haramun ne mutum ya yi amfani da shi ko ya sha shi, don Annabi (S.A.W) ya hana, ya haramta shi.
Ya ce saboda haka tunda likitoci sun bayyana cewa wannan abu na gusar da hankali, to haramun ne, kuma wajibi ne a guji amfani da shi. Imam Ibrahim ya shawarci iyaye da su kara kula da irin mutanen da ’ya’yansu suke mu’amala da su.
Sai ya yi misali da cewa: “Ruwa baya kuna, amma in aka hada shi abota da wuta to abin da wuta za ta yi maka, ruwan zafi zai iya yi maka fiye da haka wajen kuna.”
Malamin ya hori matasa da su kara himma wajen neman ilimi, su koyi sana’o’in dogaro da kai, ko karanta littattafai masu amfani.
Ya ce ya kamata su yi abota da mutanen kirki wadanda za su rika ayyukan nishadi mai kyau tare, sannan su rika zama tare cikin jama’a ta gari da shiga kungiyoyin matasa masu amfani a unguwa da cibiyoyin kyautata rayuwar al’umma.
‘Maganin basir yake mana’
Binciken Aminiya ya gano cewa, a halin yanzu a Jihar Sakkwato, a-kuskura ya zama hadari a tsakanin mutane, ganin yadda tsofaffi a cikin al’umma ke neman sa, domin su kuskura ruwa a jallo sabanin sauran kayan maye da aka san sun kebanta ne ga matasa kadai.
Wani da yake shan a-kuskura ya yi wa wakilinmu bayanin cewa, “ni ina shan a=kuskura ne domin maganin basir, kuma bai taba bugar da ni ba. Duk lokacin da na kuskura zuwa wani dan lokaci zai kada min ciki, in je, in shiga bayi, in fitar da datti. Haka nake yi lokaci-lokaci, wani sirrinsa da na gano shi ne, kana kara kuskurar sa kana kara jin karfin jikinka.”
Ya kara da cewa, “marfin kwalbar nake cikawa sai in kuskura, wani zubin ina hadewa, amma ba ko yaushe ba. Sai dai yanzu an daina samun sa a ko’ina, amma dai mun san in da ake samu, yanzu ya yi tsada, ana sayar da kwalba Naira 1,000 sabanin baya da bai yi wuyar samu ba’’.
Da yake amsa tambayar ko ba ya ganin a-kuskura yana da matsala ga lafiyarsa? Sai ya ce, “ban ganin haka, domin ni lafiya yake kara mini. Idan na sha zan ji karfi a jikina, basir da ke damu na, na raguwa sosai, in dai ina samu zan ci gaba da sha gaskiya.”
Wani bai son a ambaci sunansa, wanda kuma a da aka taba yaudarar sa, ya yi kurkura ya ce, “abokina ne yake gaya mini cewa, in ina son maganin basir in kuskura zai yi mini aiki. A ranar da na fara kuskurawa na fi awa daya ban san me nake yi ba. Take na ga kasa na juyawa da ni, a haka aka dora ni kan babur na tafi gida daga lokacin ban kara yi ba.”
Ya ce, a da shaken hanci yake, amma sai ya yanke shawarar zai gwada Aa-kuskura, ya gani ko zai yi masa maganin basir da ake fada. “Na saye shi, na tafi gida, na cire tufafina na zauna a dakina. Sannan sai na kuskura, in takaita maka magana daga nan sai na ji wani tsam tun daga kan farce na babba har zuwa kwakwalwata, na dade kwance kamar gawa. To tun daga wannan lokacin sai na koma, na ci gaba da shakena kadai, ban sake yin kuskure ba.”

Hukumar NDLEA na farautar masu sayarwa a Abuja
Wani matashi mai suna Nura Idris da ke yankin Birnin Tarayya Abuja ya bayyana sinadarin a matsayin ruwan magani da ke yi wa jiki caji, inda ake zuba shi a iya baki kawai, a kuskura shi na mintuna kamar biyar.
Ya ce, wanda ke ta’amalli da kwayoyi idan bai kasance mai karfin gaske ba, yana iya kai shi ga hararwa nan take.
Ya ce, wani abu game da sinadarin shi ne, yana kawar wa mai ta’ammali da shi sha’awar shan hayaki, musamman sigari, ta hanyar kawar da sha’awarta.
Ya bayyana direbobin manyan motaci a matsayin wadanda ke gaba wajen ta’ammali da shi. Matashin ya ce, maganar gaskiya ba abin alheri da sinadarin ke haifarwa ga jiki da ya wuce cutarwa, ta hanyan shige masa sassan jikinsa kamar kwakwalwa.
Matashin ya bayyana cewa, “a-kuskura na kama jiki sosai kuma yana sa mutum bukatar kuskurwar a-kai-a-kai, tamkar dai mai mu’amala da sigari’’.
Ya ce, a-kuskurawar kadai yana iya jijjiga mutum ta kai shi ga sai an yi masa karin ruwa.
Nura Idris ya ce, jami’an hukumomi da ke yaki da miyagun kwayoyi na farautar masu sayar da sinadarin tare da daukar mataki mai tsauri a kansu, kwatankwacin yadda a ke dauka a kan masu hulda da kwaya irin na koken.
Haka shi ma wani da Aminiya ta zanta da shi mai suna Garba Babba ya ce, an taba gabatar masa da sinadarin a matsayi maganin basur, kamar yadda a ka ce, yana maganin ciwon hakori da wasu cututtukan daban.
Ya ce, sinadarin na fitar da wasu daga cikin hayyacinsu nan take da ke kai ga sai an yi wa mutum karin ruwa.
Ya kuma kara cewa, yana shan sinadarin ne a matsayi maganin basur, amma sai ya ji cikinsa yana ta sakewa ga kuma yanayin jin jiri da sa mutum tamkar ya suma.
“Ranar da na fara kuskurawa, na tambayi wadanda nake tare da su inda nake, inda su ka shaida mini cewa, kana nan inda kake,” in ji shi.
Malam Garba Babba ya ce, ya kuma shaida yadda wani dattijo ya fita hayyacinsa nan take bayan kuskura sinadarin, lamarin da ya kai ga sanya shi a cikin baro, aka kuma garzaya da shi zuwa asibiti tare da yi masa karin ruwa.
Yadda yake illata koda da kwakwalwa —Masana
Wakilin Aminiya a Abuja ya zanta da wata kwararriya a bangaren Kula da Kiwon Lafiyar Al’umma, Dakta Mairo Mandara, inda ta ce asalin a-kukura da ta sani yana dauke da sinadarin da ake kira analgesic, wanda ke rage radadin ciwo irin na hakori idan aka yi amfani da shi.
Sai dai ta ce, bayanin da ake samu a yanzu shi ne yawanci ana jirkita shi da karin wasu sinadaran da ke kai mutum ga fita hankalinsa, irin su sinadaran wiwi ko hodar ibilis. Ta bayyana wadannan sinadaran a matsayin wadanda ke zame wa mai amfani da su jarabar rashin iya daina ta’ammali da shi.
Dakta Mairo Mandara ta ce, sinadarai ne da ke taba kwakwalwar bil’adama tare da sa shi yin halayya irin ta ’yan kwaya.
“Har ta kai ga wasu suna jin ba za su iya rayuwa ba, har sai sun yi ta’ammali da sinadarin,” in ji likitar.
Ta ce, maganin yakan yi matukar tasiri ne nan take, saboda yana shiga ta fata mai laushi da ke cikin baki da ke da tarin magudanan jini, musamman a karkashin harshe. Wannan ke sanyawa cikin gaggawa sinadarin ya kai ga jini, ya kuma karade ko’ina nan take.
“Shi ya sa a wani zubin za ka ga likitoci a asibiti na bukatar majinyaci ya sa wani maganin a karkashin harshensa na wani lokaci har ya narke a wajen, sannan ya shiga jikin mutum nan take,” in ji likitar.
Dakta Mairo Mandara ta kuma bukaci al’umma da su yi taka-tsantsan wajen ta’ammali da magunguna. Ta ce, “Kamata ya yi a tabbatar da cewa likita ne ya rubuta su, sannan da zarar an gama amfani da su kan lokacin da aka kayyade, sai a tsayar da hakan.
“Rashin bin ka’idar magunguna na daga cikin abin da ya jawo yawaitar ciwon koda a kasar nan, ga kuma uwa-uba kwaya, wadda take da karin illoli da suke haifar ta ciki har da kai mutum ga rasa kwayar halittarsa ta haihuwa a bangaren mazantaka ko matantaka.”
Likitar ta kuma bayyana takaici bisa matsalar shaye-shaye ke kara muni a kasar nan, musamman a yankin Arewa. Ta ce idan matsalar ta ci gaba a haka ba tare da an dakile ta ba, to akwai fargaban cewa yankin na iya rasa makomarsa dungurugum a nan gaba.
A nasa bangaren, Dakta Ayuba Abdurrazak, masanin magunguna a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, ya bayyana Kurkura a matsayin wani sinadari da ake amfani da shi ba bisa ka’ida ba domin maye.
Ya ce yawan amfani da shi na iya lalata hanta da koda, tare da haifar da matsalolin tunani da gazawar koda.
“Yana da illa ga hanta da koda, kuma yana iya janyo matsalolin tunani da lalacewar koda idan aka yi amfani da shi fiye da kima,” in ji shi.
Dakta Abdurrazak ya bukaci hukumomin da suka dace su dauki matakan sa ido da takaita sayar da wannan magani, domin kauce wa wata sabuwar matsalar lafiya a cikin al’umma.
Bala Gadanga, Jami’in Kiyon Lafiya a Jihar Sakkwato wanda ya kai matakin Darakta a Jami’ar Kimiya da Fasaha ta SAISA a Sakkwato, ya ce: “A-kuskara wani nau’i ne na guba. Akwai na ruwansa da na gari, wanda mutane ke amfani da shi. Wannan a-kuskura hade-hade ne na guba da ake hada wasu ganyayyaki kamar ganyen taba da ganyen wiwi da sauran wasu ganyayyaki masu guba don samar da sinadarin a-kuskura.
“Saboda haka ne Hukumar NDLEA ta haramta shi, domin hadarin da yake da shi. Yana haifar da matsalar kwakwalwa da sanya jiri. Yana kuma sanya gyambo, haka kuma idan mutum ya dade yana shan sa zai iya taba masa hanta ko kodarsa.”
Wani likita a Asibitin kwararru da ke Bauchi, Dakta Bala Shehu, ya ce a-kuskura yana da illa ga rayuwar matasa, saboda yana matukar cutar da lafiyar kwakwalwa da jiki, inda yake janyo hauka, tashin hankali da kuma kamuwa da muguwar lalura.
Dakta Shehu ya ce: “Duk abin da yake janyo matsalar kwakwalwa ka sani fa yana janyo tabin hankali na wucin-gadi ko na dindindin, da kuma sa tsananin fargaba. Sannan yana fitar da mutum daga cikin hayyacinsa ya zama guba.
“Shi kuma fita daga hayyaci yana sa mutum ya kasa sarrafa kansa, wanda hakan kan iya kai shi ga aikata laifuka ko zama mai aikata barna a cikin al’umma.”
Ya kara da cewa: “A-kuskura yana jawo matsalar lafiya ta hanyar lalata tsarin jiki da haddasa dogaro ga sinadaran da ke shafar lafiya, ya lalata kwakwalwa.”
Sai ya ba da shawarar cewa: “Ya kamata a maimakon amfani da irin wadannan abubuwa, matasa su mayar da hankali wajen wartsakar da kwakwalwa da jiki ta hanyoyin da suka dace kamar motsa jiki ta yin wasanni irin su kwallon kafa, kwallon dawaki ko kwallon hannu da sauransu. Haka kuma matasa za su iya gudu, tafiya ko zuwa dakin motsa jiki.
Gargadin Hukumar NDLEA
Kwamandan Shiyyar Zariya na Hukumar Hana Sha da Fataucin Muggan kwayu ta kasa (NDLEA), Nuhu Ahmed, ya bayyana cewa kuskure wani sinadari ne wanda ke da matukar tayar da hankali. Ana shan sa domin buguwa, wadda kan sanya masu ta’ammali da shi su rika yin wasu dabi’u marasa kyau.
“A hukumance idan muka sami irin wannan sinadari na a-kuskura sai mu tura zuwa cibiyar bincikenmu domin a san matsayinsa. A-kuskura na zuwa a nau’ika daban-daban, don haka sai bayan an kammala gwajin ne mu san takamaiman abin da ya kunsa, sannan muke sanin matakin da za mu dauka a hukumance,” in ji shi.
Ya kara da cewa: “Misali, idan a cikin wani kuskure aka samu sinadarin tabar wiwi ko tiramadol ko wata kwaya da doka ta haramta, to ko shakka babu za a hukumta duk wanda aka kama yana hadahadarsa. Amma in ba a sami wani daga cikin sinadaran da aka yi doka a kansu ba, hukumarmu ba za ta iya gurfanar da su a gaban kotu domin a hukunta su ba.”
Kwamanda ya kara da cewa dokar ta ba hukumarsu damar kama irin wadannan sinadarai domin su gudanar da gwaje-gwaje a kansu.
Kwamandan ya ce: “Akwai ci gaba sosai saboda mun bude ido, muna kuma saurare ko ta ina. Da zarar mun samu bayanin sirri kan cewa a wuri kaza akwai a-kuskura, sai jami’anmu su dira wurin saboda su dakile yadda ake cutar da al’umma.
“Babban sakonmu ga al’umma shi ne, duk abin da zai cutar da al’umma ya zama haramun, kuma ya zama wajibi a kauce wa ta’ammali da shi. Abin da gwamnati ba ta so kuma addini ya yi hani a kai, to ya kamata a kiyaye shi, domin illolinsa na da dama.”
Wani jami’in Hukumar NDLEA a Bauchi da ya nemi kada a ambaci sunansa don bai samu izinin shugaban ba, ya bayyana cewa Hukumar ta dauki a-kuskura a matsayin haramtaccen abu mai hadari, bisa la’akari da yadda abun ke shafar lafiya.
Ya ce Hukumar na ci gaba da gudanar da bincike tare da kama wadanda ke kawowa da kuma rarraba shi ko sayar wa mutane.
Jami’in ya kara da cewa: “Kwanan nan an yi ta samun yaduwar irin wannan kayan maye mai hadarin gaske, wanda aka fi sani da a-kuskura, wanda ake yin sa da tumfafiya hade da ganyen wiwi da kuma ganyen taba da wasu sinadarai, wanda kuma yake yaduwa a yankin Arewaci da Kudu maso Yammacin Nijeriya.
“Saboda hadarinsa, wasu lokutan a-kuskura yana kai mutum ga gargarar mutuwa, saboda tsananin karfin sinadaran da aka hada shi da su.
“daya daga cikin illarsa ga dan-adam bayan ya sanya mutum ya yi maye, yana kuma sanya mai sha amai da gudawa. Idan ma mutum bai saba ba, har karin ruwa da jini ake yi masa idan suka kuskura wannan kayan maye.”
Jami’in ya ce a-kuskura nau’in miyagun kwayoyi ne da ake kira sababbin sinadaran gusar da hankali, (NPS).
Sai dai Aminiya ta gano duk da cewa yana da illoli ga lafiyar dan-adam kuma yana dauke da sinadaran maye da suka hada da wiwi da sauransu, a-kuskura ana samun sa a tsakanin masu sayar da maganin gargajiya a garuruwa daban-daban a matsayin magani.
Masu sayar da shi sukan yi karyar cewa yana maganin sanyi, mura, tari, ciwon kai, hawan jini, ciwon suga, karin kuzarin mazakuta, ko maganin amosani, kasala da gajiya.
A zahirin gaskiya, babu wani ingantaccen nazari da masana suka yi wanda ya tabbatar da yakinin cewa A-kuskura na maganin ko da daya daga cikin wadannan cututtuka.
Abin da bincike ya tabbatar shi ne, A-kuskura sinadari ne na kwaya wanda hukuma ta haramta amfani da shi. Wannan kuwa yana nuna cewa duk mai sayar da shi yana taka doka ne, kuma zai iya gamuwa da fushin hukuma, haka ma wanda yake sha da wanda yake safarar sa..
A Kudu ake hadawa a kawo Arewa —Hukumar NDLEA
A zantawarsa da Jaridar Aminiya, Babban Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun kwayoyi na Abuja, wato NDLEA, Mista Femi Babafemi ya ce, a bincike da su ka gudanar tun bayan bayyanar sinadarin a shekarar 2023, sun gano cewa, an fi sarrafa sinadarin ne a Ibadan Babban Birnin Jihar Oyo, da ke a yankin Kudu maso Yammacin kasar nan.
Sai kuma Jihar Kwara da ke makotaka da Jihar ta Oyo da ke biye mata, da ke a yankin jihohin Arewa ta Tsakiya, kamar yadda ya ce, aikinsu na sumame da kuma kame a kan matsalar ya nuna.
Baban Jami’in na Hukumar ta NDLEA ya ce, bayan an sarrafa sinadarin a wadannan jihohin biyu, yawanci a na safarar sa ne zuwa jihohi kamar Kano da Jigawa da Kaduna, da ke yankin jihohin Arewa maso Yamma.
Ya kara da cewa, masu hada sinadarin na ikirarin cewa, magani ne na gargajiya. Amma a bisa tsari bai kamata yana dauke da wani kalubale ga lafiya ba.
Sai dai, a cewarsa binciken da suka yi a kan sinadarin a dakinsu na gwaji ya nuna cewa, yawanci ana surka a-kuskura ne da sinadarai masu sa maye a yayin hadi da ya hada da na ganyen wiwi da kuma sinadarin OPIUM da dai sauransu.
Ya ce, babu matsala ga wadanda nasu bai kunshi munanan sinadaran ba, saboda bai saba dokar kasa ba.
Amma ya ce, wadanda suka saba doka su ne wadanda suka surka nasu da miyagun kwayoyi inda ya ce, hukumar ke daukar tsauraran matakai a kan ma’abotansa da ya hada da kama su da gurfanar da su a gaban kotu, sai kuma ruguza inda ake aikin da kuma abubuwan da a ke amfanin da su wajen sarrafa shi.
Daga Ibrahim B. Surajo da Adam Umar, Abuja da Aliyu Babankarfi, Zariya da Ahmed Mohammed, Bauchi da Nasiru Bello, Sakkwato