A kwato hakkinmu kafin zaben 2015

Mata da maza, yara da manyan dalibai da malamai, har da na jami’a da ma’aikatan lafiya da wadanda ba sa aiki da ‘yan fansho, har da jami’an tsaro da ba a biya hakkinsu da wadanda aka rufe ko aka sayar da kamfanonin gwamnati da suke aiki, suka rasa aikin, da kananan ‘yan kasuwa kowa ya […]

A kwato hakkinmu kafin zaben 2015
A kwato hakkinmu kafin zaben 2015

Mata da maza, yara da manyan dalibai da malamai, har da na jami’a da ma’aikatan lafiya da wadanda ba sa aiki da ‘yan fansho, har da jami’an tsaro da ba a biya hakkinsu da wadanda aka rufe ko aka sayar da kamfanonin gwamnati da suke aiki, suka rasa aikin, da kananan ‘yan kasuwa kowa ya fito ya gaggauta bayyana wa duniya goyon bayansu da hadin kansu garemu, har sai an kwato mana hakkinmu daga hannun dukkan wadanda suka wawushe mana arzikin kasa, suka talautamu, suka jefa mu cikin jahilci da cututtuka da rashin tsaro, kafin kowanne irin zabe da za’ayi nan gaba.
kowa ya sauka a kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin alkalin-alkalan Najeriya. Duk Wanda bai taimaka mana ba, to bakinsu daya da azzaluman shugabani,.su ma sai an binciki yadda suka samu damar da duk sauran mutane ba su iya samu ba, sai su da masu mulki.
Tunda Jonathan ya zama shugaban kasa bai iya gudanar da bikin samun mulki da aka saba yi duk shekara ba, saboda rashin tsaro, Allah kadai yasan rayukan da suka salwanta a mulkin Ebele Jonathan; ya yi amfani da Attahiru jega, ya yi amfani da mataimakan shugabanni da malaman jami’a wajen zabuka duk ya ga wallensu, ya raina hukumar shari’a, tunda ya yafe wa Alamisiya duk laifukan da ya yi, ya mayar masa dukiyar da ya sata, ga shi kotunan Nageriya sun kasa daure James ibori sai da ya je Ingila, inda ya kai dukiyar da ya sace mana, aka daure shi.
Ga wadanda suka sace mana tiriliyon biyu da biliyan 700 (N2.7 tril) na tallafin mai ba a kwato mana ba balle a hukuntasu.
Ga ministan Shari’a cikin matsalar  $1.3bn (Don Etete malabu oil). Ga Dala biliyan 49 da miliyan 800 na mai Wanda ba’a shigar da su Baban Bankin Najeriya ba, ga wasikar da Obasanjo ya rubuta wa Jonathan mai shafi 18.
Haka za mu zuba ido a yi tayi mana sata ana kashemu, mun kasa yin komai, sai ka ce dabbobin gida? Wacce irin adawa ce kullum jiran tsammani?
Gwamnatin rikon kwarya ya zama dole idan ba so ake mu dawwama a haka ba, kamar yadda wasu suka dauka, haka aka halicce su, haka za su rayu,haka za su mutu. saboda raunin imani da kwadayi da tsaro. Ba sa tsoron Allah sai mai mulki! ba duk aka taru aka zama daya ba. idan wasu ba su sani ba, ko sun manta yadda aka kori Turawan nulkin mallaka na ingila daga Najeriya, aka samu mulkin kai, aka maida dukkan sarakunan karkashin talakawa.
Mun kori sojaji daga mulki, duk da sojojin sun mamaye harkar mulki da siyasa, suma sai an yi garambawul akansu, domin hana yin mulkin karba-karba irin na soja.
Kowa dai yana jin irin abubuwan da suke faruwa yanzu a wasu kasashe na duniya ta kafafen watsa labarai na duniya, koma suna gani a talabijin. Na baya-bayannan su me, Thailand da Ukraine. Mu ma mutane ne kamar su, a kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin Alkalin-Alkalan Najeriya. A kwato mana duk abin da aka sace mana, a hukunta barayin a bainar jama’a. Sannan a kafa harsashin mulkin adalci tsantsa. Ba sai mun jira abin da ya faru a Ghana ya faru a Najeriya ba.To mu dai gamu ga Allah! Duk wanda ba ya jin tsoron Allah, bai kamata mutane suji tsoronsa ba balle ma a ji kunyarsa. Duk abin da yake tinkaho da shi Allah ya fi shi, kowanene shi, ko dan wanene. Allah shi ne kadai abin tsoro.                                      
Idan ban da lallacewa a ce sojan Najeriya ya fito kafar yada labarai ta BBC Hausa a ranar 19-8-2014 yana gaya wa duniya cewa an turasu yaki da yan’boko haram, amma ba su da bulet ko daya a bindigarsa. Don Allah da lallacewar da tafi wannan ballantana uwa uba talaka, wanda ko wukar arziki ba shi da ita; duba irin wannan wai ake ta kururuwar a na tsaro. Allah ya kyauta.
kololuwar zalunci shi ne:
1.Hukuma ta rika kashe mutane ko raunata su ba tare da yi musu shari’a a kotuna ba.
2.Hukuma ta gaza kare rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addinin al’ummar ta.
3.Shin nawa ne a ke biyan iyalin ma’aikatan gwamnati hada da soja ko dan sandan da a ka kashe su a wajen yaki? Shin wacce irin kulawa a ke bai wa iyalin dan sanda ko sojan da ’yan Boko Haram ko Ombatse suka kashe a matsayinsu na wadanda suka rasa masu daukar dawainiyarsu a rayuwa? Shin muna ji a ranmu kuwa a lokacin Jonathan akwai wani soja mai hankali da zai iya sadaukar da rayuwarsa saboda kasar nan?
A yanzu dai abin da muka fi ji shi ne, bai wa masu aikata laifuka rigar kariya ta ‘amnesty,’ amma ba biyan diyyar ma’aikatan tsaron da suka rasa rayukansu a yayin fadda da wadancan makasa ba. Me ya sa? Wadannan su ne abubuwan da suka kamata mutattauna a kansu a irin wannan lokaci da tsaron cikin gida ya tabarbare.
Gwamnati ta gaza kwato dukiyar talakawa da masu mulki suka wawushe da karfin mulki. An bar talakawa cikin matsanancin talauci da yunwa da cututtuka, ba tare da kowane irin tallafi ba. Mutum daya ya saci Naira miliyan dubu, ana ganinsa a kyale shi, ga talakawa miliyan, babu Naira dubu. Allah ya rusa zalunci da azzalumai!

Anas Saminu Ja’en Makera, Jami’in Hulda da Jama’a a kungiyar Muryar Talaka, Reshen Jihar Kano. 07033882307,07033882307.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya