A kwato mana hakkinmu kafin zaben 2015

Mata da maza, yara da manya, dalibai da malamai har da na jami’a da ma’aikatan lafiya da wadanda ba sa aiki da ‘yan fansho, har da na jami’an tsaro da ba a biya hakkinsu da wadanda aka rufe ko aka sayar da kamfanonin gwamnati da suke aiki, suka rasa aikin, da kananan ‘yan kasuwa kowa […]

A kwato mana hakkinmu kafin zaben 2015
A kwato mana hakkinmu kafin zaben 2015

Mata da maza, yara da manya, dalibai da malamai har da na jami’a da ma’aikatan lafiya da wadanda ba sa aiki da ‘yan fansho, har da na jami’an tsaro da ba a biya hakkinsu da wadanda aka rufe ko aka sayar da kamfanonin gwamnati da suke aiki, suka rasa aikin, da kananan ‘yan kasuwa kowa ya fito ya gaggauta bayyana wa duk duniya goyon bayansu da hadin kansu garemu, har sai an kwato mana hakkinmu daga hannun dukkan wadanda suka wawashe mana arzikin kasa, suka talautamu, suka jefa mu cikin jahilci da cututtuka da rashin tsaro, kafin kowanne irin zade da za a yi nan gaba.
Kowa ya sauka a kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin alkalin alkalan Najeriya. Duk wanda bai taimaka mana ba, bakinsu daya da azzaluman shugabannin. Suma sai an binciki yadda suka samu damar da duk sauran mutane ba su iya samu ba, sai su da masu mulki.
Tunda Jonathan ya zama shugaban kasa bai iya gudanar da bikin samun mulki da aka saba yi duk shekara ba saboda rashin tsaro, Allah kadai yasan rayukan da suka salwanta a mulkin Ebele Jonathan, ya yi amfani da Attahiru Jega, Jega ya yi amfani da mataimakan shugabanni da malaman jami’a wajen zabuka duk ya ga wallensu, ya raina su baki daya. Ya raina ‘yan majalisun tarayya sun kasa yin komai, ya raina hukumar shari’a, tunda ya yafe wa Alamisiya duk laifukan da ya yi, ya mayar masa dukiyar da ya sata ga shi kotunan Najeriya sun kasa daure James Ibori sai da ya je Ingila, inda ya kai dukiyar da ya sace mana, aka daure shi.
Ga wadanda suka sace mana tiriliyon biyu da biliyan 700 (N2.7 tril) na tallafin mai ba a kwato mana ba balle a hukuntasu. Ga Ministan Shari’a cikin matsalar $1.3bn (Don Etete Malabu Oil). Ga Dalar Amurka $49.8bn na mai wanda ba’a shigar dasu CBN ba, ga wasikar da Obasanjo ya rubutawa Jonathan mai shafi 18.
Haka za mu zuba ido a yi tayi mana sata ana kashemu, mun kasa yin komai, sai ka ce dabbobin gida? Wacce irin adawa ce, kullum jiran tsammani? Gwamnatin rikon kwarya ya zama dole idan ba so ake mu dawwama a haka ba, kamar yadda wasu suka dauka, haka aka halicce su, haka za su rayu, haka za su mutu. Saboda raunin imani/kwadayi da tsoro. Ba sa tsoron Allah sai mai mulki! Ba duk aka taru aka zama daya ba. Idan wasu ba su sani ba, ko sun manta yadda aka kori Turawan mulkin mallaka na Ingila daga Najeriya, aka samu mulkin kai, aka maida dukkan sarakuna karkashin talakawa.
Mun kori Sojoji daga mulki, duk da Sojojin sun mamaye harkar mulki da siyasa, suma sai an yi garambawul akansu, domin hana yin mulkin karfa-karfa irin na Soja. Kowa dai yana jin irin abubuwan da suke faruwa yanzu a wasu kasashe na duniya ta kafafan watsa labarai na duniya, koma suna gani a talabijin. Na baya-bayan nan su ne, Thailand da Ukraine. Mu ma mutane ne kamar su. Mafi sauki da zaman lafiya, shi ne, duk wadanda aka zaba su sauka ko a sauke su, a kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin Alkalin-alkalan Najeriya. A kwato mana duk abin da aka sace mana, a hukunta barayin a bainar jama’a. Sannan a kafa harsashin mulkin adalci tsantsa. Ba sai mun jira abin da ya faru a Ghana ya faru a Najeriya ba.
                                                
                                                                                                                          

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno