A kyale Gwamnan Neja ya yi wa jama’a aiki – Shugaban APC
Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Neja Injiniya Muhammad Jibrin Imam ya shawarci abokai da makusantan Gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bello su kyale shi ya yi wa al’ummar jihar da suka zabe shi aiki ta yadda zai cika musu alkawuran da ya yi musu a lokacin yakin neman zabe.Injiniya Muhammad Imam ya bayyana haka ne […]
Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Neja Injiniya Muhammad Jibrin Imam ya shawarci abokai da makusantan Gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bello su kyale shi ya yi wa al’ummar jihar da suka zabe shi aiki ta yadda zai cika musu alkawuran da ya yi musu a lokacin yakin neman zabe.
Injiniya Muhammad Imam ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da wakilin Aminiya a Mina inda ya ce lokaci ya yi da wadannan mutanen za su bar Gwamna Abubakar Sani Bello ya ba bukatun al’ummar da suka zabe shi kulawar da ta kamata musamman samar musu muhimman ababuwan more rayuwa.
Shugaban Jam’iyyar wanda ya nuna cewa wannan ce babbar damar da suka samu da za su nuna wa mutanen da suka zabe su salon mulki na gaskiya, ta yin amfani da kudinsu don samar wa ’ya’yansu ingantaccen ilimi da kiwon lafiya da tsabtataccen ruwan sha a birane da karkara.
Imam ya ce matukar abokai da makusantan Gwamnan ba su bar shi ya yi wa jama’a aiki ba, abin da ya samu Jam’iyyar PDP da ta share shekara 16 tana mulki a jihar zai same su, kuma da wuya su sake samun irin wannan dama.
Ya bayyana halin da jihar take ciki da cewa babban abin takaici ne idan aka yi la’akari da dimbin albarkatun da Allah Ya yi mata da makudan kudin da ta samu, amma mutane kalilan sun zame wa jihar karfen kafa sun hana ta ci gaba kamar takwarorinta da aka kirkiro su tare a 1976.
Shugaban ya yaba wa jama’ar Jihar Neja da suka sake fitowa suka zabi shugabannin kananan hukumomin da jam’iyyar ta tsayar takara.
Ya ce tuni suka fitar da duk wanda aka zaba a karkashin jam’iyyar zai yi wa jama’a aiki ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba. Ya shawarci wadanda aka zaba su rika kasancewa tare da mutanensu daga lokaci zuwa lokaci suna sauraren koke-kokensu tare da tsara hanyoyin da za a magance su.