A makon da ya arce ne jaridu da mujallun qasar Haurobiya suka baje wa Haurobiyawa wata maqala da Farfesa Sallu-Lado ya gabatar a wajen taron bikin wata mujalla a birnin Ikko ikon Allah. Maqalar wannan masanin tsimin alkinta dukiya da tattalin tallafar tal
A makon da ya arce ne jaridu da mujallun kasar Haurobiya suka baje wa Haurobiyawa wata makala da Farfesa Sallu-Lado ya gabatar a wajen taron bikin wata mujalla a birnin Ikko ikon Allah. Makalar wannan masanin tsimin alkinta dukiya da tattalin tallafar talalar talauci, ya yi ta ne a kan tsarin tsimi da tanadi na […]
A makon da ya arce ne jaridu da mujallun kasar Haurobiya suka baje wa Haurobiyawa wata makala da Farfesa Sallu-Lado ya gabatar a wajen taron bikin wata mujalla a birnin Ikko ikon Allah. Makalar wannan masanin tsimin alkinta dukiya da tattalin tallafar talalar talauci, ya yi ta ne a kan tsarin tsimi da tanadi na Baban-Burin-huriyya da ke jan ragamar kasar nan a karkashin tutar Jam’iyya mai maganin zugi da radadin ciwon kurungu. Da na yi bitar wannan makala sai na fasko cewa, ya yi ta ne kawai a kan wasan Samson siya-siya da ake yi wajen jan ragamar al’ummar Haurobiya.
Farfesa Sallau-Lado dai har Gwamna gwarangwam na babban asusun Haurobiya ya taba zama, har ma ya cakume Hauro, inda ya goge mata zanenta na ajami. Ganin cewa, ya koda Baban Burin-huriyya, ya kuma caccaki Jona-tanti da Gudun-loko da Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta aiwatar mana tsawon shekaru manuniyar sama, sai in ce ya yi rawar gani, amma bai yi katabus ba. Domin baicin irin zakuwar Haurobiyawa na ganin an warware musu kullin tufkar ta’asar kwanon tasa da aka assasa musu, ai sai in ce, mulkin watanni manuniyar sama ba daidai yake da na shekaru sili da manuniyar sama ba.
Salon Sallau-Lado dai yana sauyawa kamar na hawainiya, domin an taba rawar banjo da shi a zamanin Baba-ojo mai gonakin Ottawa, domin ya taba gabatar da wata makala a Jam’in jama’ar jami’ar Bini-bini, inda ya yi mata taken: Ko Haurobiya za ta zamo kasar Sin din Ifrikiyya? Ya gabatar da makalar ce a rana ta karamin lauje da kofar hanci ga watan Noman-Baba na shekara ta dubu karamin lauje da manuniyar sama.
A matsayina na katafaren direban alli na farfajiyar koyon watsatttsake da buda wagagen littattafai, na fasko cewa, akwai hajijiya da wuntsulagudi-gudin masana. Kuma wani abu da ’yan makaranta ba su fasko ba, shi ne, maimakon Haurobiya ta zama Sin din Ifrikiyya, sai ta kusa karkewa da zama Sansanin sanen Ifrikiyya,’ bayan shekara sili da zagaye da Farfesa Sallau-Lado ya gabatar da makalarsa.
Wata kasassabar masana da na ci karo da ita a makalar wannan masani da ya ci farfesun ilimi, ita ce yin adawa da “burgame ko lalita guda” na adana ’yan matsabban gweamnati da wannan gwamnatin ta fito da shi. Wai a fahimtarsa bai kamata mu koma zamanin da ba, wato inda za a rika jibge damin Hauron gwamnati a Babban Asusun Haurobiya. Ko ma dai mece ce hujjarsa, na san burgame guda ko lalita guda da Baban Burin-huriyya ya bayar da umarnin adana matsabban hukuma a ciki, ya jefa samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya cikin matsanancin hali. Kuma wannan tsari na cikin jerin dabarun dabarbarta masu kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma.
Saman-dagarin samarin kusu da aka antayya a ramukan jaba da gafiya ya fara aiki, domin yau duk wanda ya duba daukacin jaridun kasar Haurobiya zai ga labarin yadda samarin kusu ke ta azarbabin dawo da damin Hauron da suka jida, kamar yadda shugaban kasa ya bayyana. Sannan ya ce akwai yunkurin fadada yaki da kwashi-kwaraf da matsabban al’umma har zuwa kan wadanda suka tafka aika-aika a garin Aikawa zamanin Baba-ojo da Marigayi Shugaba ’Yar’bishiya aka gangaro zuwa Gudun-loko da Jona-tantin mulki.
’Yan makaranta, ya kamata ku fasko cewa, damman da samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya suka mayar cikin lalitar kwasar Haurobiya, da su za a harhada a tara tiren-taliya tukunyar dambu da Usainin-Babajo ya ce za su kasafta wajen aitawar da ayyuka, ta yadda masu kwashi-kwaraf ba za su aika da Hauro zuwa Aikawa ba.
Salon Sallau-Lado na yin ludo da kwado zai bai wa al’umma damar yin jido Kwando-kwando. Kuma kada mu bari ya sake kwatanta kasar Haurobiya da kasar Sin, musamman ma ganin cewa, kasar sananniya ce a duniyar masana, amma Haurobiya ta kusa karkewa da zama ‘Sansanin masu sane,’ har sai da jam’iyyar mai tsintsiyar laushi da ta kwakwa suka yunkuro wajen kawar da mai dan boto da shafe shekaru tana jirga Haurobiyawa. Kuma tana shirin magance zogi da radadin ciwon kurungu da ya kama Haurobiya. Hasalima kwanan nan shugaban kasar nan ya salami Loma-a-murde, inda ya maye gurbinsa da mugun madambaci Iro Mugun da ya hana miyagu magu-magu. Duk wannan wata loga ce ta kange masu tatuke lalitar Haurobiya, har su zo suna ihun cewa, wai ba za su iya biyan ladar kwadagon neman kadago mafi karanci na dubu sili da madambaci ba.
Sallau-Lado nisan shekaru da tarihi na koyar da masu hankali a kwanyarsu babban darasin tunkarar kowace irin matsala da ke ci wa al’umma tuwo a kwarya. Don haka nike da tabbacin cewa kasar Sin ba ta zama Sinu ba, sai da tarwatsa sansanin sanen cikinta. Mu ma a halin yanzu al’amarin da ake fafutikar aiwatarwa ke nan.
Lokaci ya yi da masana za su himmatu wajen inganta dabarun toshe ramukan samarin kusu, ba wai adawa da burgame ko lalita guda ba. Domin wannan tsari da shugaban kasar Haurobiya ya fito da shi, matukar ya yi aiki a da, to yanzu za a iya daidaita shi da zamani, ta yadda al’ummar kasa za su amfana. Sannan dole ne a kai rahoton kowane asusun ajiyar Hauron Haurobiyawa da ke tallafa wa ta’asa a kwanon tasa. Na ja na-zomon asusu mai mangalar hauro da ke da tambarin giwa da mabudin dutse da Uba mai tarairayar dukiyar ’ya’yansa da Asusun assasa korar kaza na as!as!as! da mai hada kai a tsallen ingarma da sauransu, kan lallai su yi taka-tsantsan wajen bin ka’idar da aka shimfida ta hada-hadar sarrafa Hauro, don samun fa’ida tururu. Shi kuwa farfesa Sallau-Lado da ya soki lamirin tsarin adana Hauron Hukuma a Burgame guda, to ya himmatu wajen binciko tsari mafi alfanu na alkinta Hauro, ta yadda samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya ba za su samu kafar yi mana wa-ka-ci-ka tashi ba!