A makon gobe Super Eagles za ta fara wasanta na farko a karkashin Sunday Oliseh
A ranar Asabar 5 ga Satumba ne kungiyar kwallon kafa ta kasa wato Super Eagles za ta hadu da Tanzaniya a Dar es Salam. Wannan shi ne zai kasance wasan farko ga sabon koci Sunday Oliseh.Wasan ne na neman gurbin hayewa gasar cin kofin Afirka. Wannan shi ne wasa karo na biyu bayan wanda kungiyar […]

A ranar Asabar 5 ga Satumba ne kungiyar kwallon kafa ta kasa wato Super Eagles za ta hadu da Tanzaniya a Dar es Salam. Wannan shi ne zai kasance wasan farko ga sabon koci Sunday Oliseh.
Wasan ne na neman gurbin hayewa gasar cin kofin Afirka. Wannan shi ne wasa karo na biyu bayan wanda kungiyar ta fafata da Cadi a garin Kaduna a watan Yunin da ya wuce. A wancan lokaci, tsohon kocin kungiyar Stephen Keshi ne ya jagoranceta.
Wasan zai gudana ne da misalin karfe 2 da rabi na rana agogon Najeriya kamar yadda wata sanarwa da Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta fitar a yanar sadawarta a ranar Talatar da ta wuce.
Hukumar NFF ta ce ta samu sakon lokacin da wasan zai gudana na karfe biyu agogon Najeriya ne daga wajen Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Tanzaniya Jamal Malinzi.
Sannan ana sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta hadu da kungiyar kwallon kafa ta Nijar a garin Fatakwal a wani wasan sada zumunta da zarar ta dawo gida daga Tanzaniya. Wasan zai gudana ne a ranar Talata 8 ga watan Satumbar nan da muke ciki.
Kawo yanzu kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ce ta biyu a rukunin G bayan ta lallasa Cadi a garin Kaduna da ci 2-0. kasar Masar ce take kan gaba a rukunin bayan ta lallasa Tanzaniya da ci 3-0.
Tuni kocin Super Eagles ya gayyato ’yan kwallon da yake ganin za su fafata a wasan, kuma ya hore su da su yi taka tsan-tsan da Tanzaniya don wasa ne da za su dage don ganin sun samu nasara a kan Najeriya musamman ganin cewa sun yi rashin nasara a wasansu na farko da Masar. Ita kuma Najeriya za ta yi kokarin ganin ta samu nasara a wasan ne don ta hada maki 6 kafin ta hadu da Masar a wasa na uku.
Ana sa ran kungiyoyi biyu ne daga kowane rukuni za su hayewa zuwa gasar cin kofin Afirka da zai gudana a Gabon a shekarar 2017 idan an gama wasannin share fagen.