A makon gobe za a dakatar da gasar La-Liga ta Sifen
Ana sa ran daga ranar 16 ga wannan wata da muke ciki ne za a dakatar da gasar rukuni-rukuni na La-Liga da ke Sifen saboda yajin aiki da kungiyar Mahukunta kulob din (Professional Soccer League) na gasar ke niyyar yi a dambarwar da ke tsakaninsu da Hukumar kula da kwallon kafa ta Sifen (FA) wajen […]
Ana sa ran daga ranar 16 ga wannan wata da muke ciki ne za a dakatar da gasar rukuni-rukuni na La-Liga da ke Sifen saboda yajin aiki da kungiyar Mahukunta kulob din (Professional Soccer League) na gasar ke niyyar yi a dambarwar da ke tsakaninsu da Hukumar kula da kwallon kafa ta Sifen (FA) wajen rashin yin raba daidai a kudin da ake samu na tallata gasar da gidajen talabijin na ciki da wajen kasar ke yi.
Idan haka ta faru, gasar za ta samu tsaiko na sauran wasanni uku da suka rage kenan bayan an buga na wannan mako. Haka kuma yajin aikin zai shafi wasan karshen cin kofin kalubale na Sifen (Copa del Rey) a tsakanin kulob din FC Barcelona da Athletic Bilbao a ranar 30 ga wannan wata na Mayu.
Wata sanarwa da Hukumar shirya kwallon kafa ta Sifen fitar a jiya Alhamis ta nuna cewa “za a dage wasannin La-Liga da suka rage ne da kuma na wasan karshe na Copa Del Rey daga ranar 16 ga Mayu 2015 sai illa masha Allah saboda yajin aikin da masu kungiyoyin da ke fafatawa a gasar za su fara”.
Su dai masu kungiyoyin kwallon kafa a Sifen sun samu nasara ne a karar da suka shigar inda kotun ta umarci Hukumar shirya gasar (FA) ta rika yin raba daidai a kudin shigar ake samu daga gidajen talabijin na ciki da wajen kasar amma gwamnati ta yi biris da umarnin kuma ta ce sai dai ta rika ba su wani kaso amma ba su yi raba daidai ba. Hakan ta sa kungiyar mahukunta kulob da ke gasar suka yanke shawarar shiga yajin aiki don tursasawa gwamnati ta amince da bukatarsu.
Masu sha’awar kallon gasar a akwatin talabijin a fadin duniya ciki har da Najeriya ba za su kalli gasar ba daga makon gobe har sai an janye yajin aikin.