A makon nan matsalar fetur za ta kau – Danladi Pasali

A yayin da ake fama da dogayen layIn motoci a gidajen man kasar nan, sakamakon matsalar karancin man fetur da ake fama da shi, sakataren kungiyar dillalan man fetur ta kasa, Alhaji danladi Garba Pasali ya bayyana cewa nan da karshen wannan mako za a warware wannan matsala a Najeriya. Ya bayyana haka ne a […]

A makon nan matsalar fetur za ta kau – Danladi Pasali

A yayin da ake fama da dogayen layIn motoci a gidajen man kasar nan, sakamakon matsalar karancin man fetur da ake fama da shi, sakataren kungiyar dillalan man fetur ta kasa, Alhaji danladi Garba Pasali ya bayyana cewa nan da karshen wannan mako za a warware wannan matsala a Najeriya.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu. Ya ce a taron da suka yi, an tabbatar masu  cewa akwai manya-manyan jiragen ruwa guda 6 da suka iso Najeriya, dauke da man fetur suna nan suna saukewa a Fatakwal da Legas da Warri.

“Ina tabbatar maka cewa daga nan zuwa Juma’ar nan, za a ga raguwar layin motoci a gidajen mai, domin tuni mun tura motocinmu zuwa wadannan wurare, domin su dauko mai, su kai ko’ina, musamman Arewacin kasar nan.”

Sakataren ya bayyana cewa tuni sun umurci ’ya’yan kungiyarsu wadanda suke da manya-manyan kamfanoni, su rika sayar da mai dare da rana a gidajen mansu, domin a kawo karshen wadannan dogayen layukan da ake fama da su a gidajen man kasar nan.

Ya gargadi ’ya’yan kungiyar tasu da su guji amfani da wannan dama wajen kautar da man da aka ba su, da nufin kuntata wa mutanen kasar nan. Ya ce duk wanda ya dauko mai, ya kai gidan mansa, kada ya kauce da shi, domin duk wanda ya karkatar da mai, idan aka kama shi babu ruwan kungiyar.

“Mu kanmu ba mu jin dadin wannan matsalar karancin mai da ke faruwa a kasar nan. Don haka mun tsaya don taimaka wa hukumar kamfanin mai ta kasa (NNPC) da gwamnati don kawo karshen wannan matsala,” inji shi.

Ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu kan wannan al’amari, domin a halin yanzu motocin daukar mai sun fito daga kudanci dauke da mai, zuwa kowanne lungu na kasar nan.