‘A masallacin Sultan Bello aka daura auren Sufeto Janar da amaryasa’
A masallacin Sultan Bello da ke Kaduna aka daura auren Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Ibrahim Kpotun Idris da amaryarsa Malama Asta Hassan, wacce direbar jirgin sama ce. Alhaji Lawal A. Ibrahim wanda shi ne kawun amaryar , ya shaida wa Aminya cewa: “An daura auren ne a bayyane a masallacin Sultan Bello sannan na ba […]

A masallacin Sultan Bello da ke Kaduna aka daura auren Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Ibrahim Kpotun Idris da amaryarsa Malama Asta Hassan, wacce direbar jirgin sama ce.
Alhaji Lawal A. Ibrahim wanda shi ne kawun amaryar , ya shaida wa Aminya cewa: “An daura auren ne a bayyane a masallacin Sultan Bello sannan na ba da takardar shaidar daurin auren kamar yadda ake yi a masallacin, don ba a boye aka daura auren ba kamar yadda ake zargi”
Ya ce, “an daura auren ne a ranar 15 ga watan Sataumba day a gabata a cikikn Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna kuma wadanda suka halarci duarin auren sun hada da Hon. Halliru Jika (Dokaji) Bauchi, Hon. Kontagora da jami’an ’yan sanda da sauran mutane da dama.”
Ya dara da cewa, “zargin da Senata Misau yake yi na cewa an daura auren bayan da ta samu juna-biyu batanci ne ga Sufeto-Janar da Asta Hassan da zuri’ar gidansu, domin ya kamata ne ya yi tambaya don sanin hadidanin abin da ya faru; ba ya fito yana yin zargin bata suna ga mutane ba, domin mu Musulmai ne ’yan asalin daramar Hukumar Bama da ke Jihar Borno kuma muna da mutunci da sanin addini da sunan dwarai da ya kamata mu kare. Don haka muna shirye-shiryen gurfanar da shi a gaban kotu don dwato wa kanmu mutunci daga wannan zargi.”
Da Aminiya ta tuntubi daya daga cikin shugabannin masallacin na Sultan Bello da ke Kaduna, wanda ya ce ba ya son a fadi sunansa; ya ce lallai an daura auren Sufeto-Janar Ibrahim Idris da Malama Asta Hassan ranar 15 ga watan Satumba kuma jama’a da dama sun halarta. Ya ce hukumar ta amince cewa ba za ta bayar da kwafin takardar shaidar auren ba don abu ne mallakin ma’aurata da hukumar masallaci. Ya dara da cewa ba su bin diddigi in aure ne na budurwa, amma suna neman shaidar sakin aure a rubuce ko na tsohon miji ko kuma na kotu.