A mayar da farashin man fetur N900 ko a dawo mana da kuɗinmu — IPMAN

Shugaban IPMAN ya kuma buƙaci a mayar musu da kuɗaɗen da suke bin ‘yan kasuwar mai, wanda kamfanin NNPC ke riƙe da shi tsawon watanni uku da suka gabata.

A mayar da farashin man fetur N900 ko a dawo mana da kuɗinmu — IPMAN

Shugaban Ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Ƙasa (IPMAN), Abubakar Shettima, ya buƙaci kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) da ya siyar da man fetur (PMS), ga ‘yan kasuwarsa a kan farashin da ake bayarwa ta Matatar Mai ta Dangote.

Shettima, yayin da yake bayani a ranar Alhamis a tashar Talabijin na Channels, ya kuma buƙaci a mayar musu da kuɗaɗen da suke bin ‘yan kasuwar mai, wanda kamfanin NNPC ke riƙe da shi tsawon watanni uku da suka gabata.

Ya nanata matsalar maido kuɗin da tsawaita jinkirin dawo da kuɗaɗen ya haifar wa ‘yan kasuwar man fetur, inda ya buƙaci NNPC da ta ɗauki matakin gaggawa.

“Babban ƙalubalen da ke gabanmu a yanzu shi ne, a halin yanzu, muna da bashin da NNPC ke bin mu, kuma kamfanin ya karɓii man ta hanyar matatar Dangote a kan farashi mai rahusa – da bai kai har N900 ba.

“A halin yanzu, kuɗaɗenmu suna tare da su (NNPC) kusan watanni uku,” in ji shi.

A cewarsa, kamfanin mai na ƙasa ya umurci ‘yan Ƙungiyar IPMAN da su siyo musu man a kan kuɗi N1,010 a Legas, N1,045 a Calabar, N1,050 a Fatakwal da kuma N1,040 a Warri. .

Da yake nuna rashin jin daɗinsa kan matakin da NNPC ya ɗauka na cewa ‘yan kasuwa su sayi mai kai tsaye daga matatar Dangote, Shettima ya ce: “Muna da matsala a kan hakan, domin kuwa a wurinsu muke sayen man fetur ɗin.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya