‘A mayar da harkar Hajji ga kamfanoni masu zaman kansu’

  An yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta binciki yadda Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) ta gudanar da aikin Hajjin bana, tare da gagaguta mayar wa alhazai rarar kudin da aka yin zargin cewa an zalunce su. Wanann kira ya fito ne daga shugaban Kamafanin Sufurin Jiragen Sama na Darma, Ambassada Hassan Usman Darma […]

‘A mayar da harkar Hajji ga kamfanoni masu zaman kansu’

 

An yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta binciki yadda Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) ta gudanar da aikin Hajjin bana, tare da gagaguta mayar wa alhazai rarar kudin da aka yin zargin cewa an zalunce su.

Wanann kira ya fito ne daga shugaban Kamafanin Sufurin Jiragen Sama na Darma, Ambassada Hassan Usman Darma a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya.

Darma wanda shi ne Mataimakain Shugaban Cibiyar Ciniki ta Jihar Kano, ya bayyana cewa, duk da yawan kudin da aka tatsa daga wurin alhazan, amma ba a samar musu da kyakkyawan yanayi na gudanar da aikin Hajjin ba. Baya ga wannan, ya ce alhazai sun fuskanci rashin inganci a ayyukan da aka yi musu, la’akari da irin masaukan da aka ajiye su, wadanda ke da nisan kilomita biyu zuwa biyu da rabi daga Harami. 

“A gaskiya masaukan da aka ajiye mafi yawan alhazan kasar nan sun yi nisa kwarai da gaske, yadda har alhazan ba su samun damar zuwa harami saboda nisa da kuma rashin abin hawa,” inji shi. 

Ya bayyana cewa kamata ya yi gwmanati ta yi gyara game da kwanakin da alhazai ke shafewa a kasa mai tsarki, wanda a cewarsa ya yi yawa. Ya ce hakan kuma shi ke kawo alhazan kasar suna zama mabarata saboda yankewar guzuri. “Babu dalilin da zai sa ka dauki Alhaji ka kai shi ya yi kwana 40, domin dadewar tana janyo wa alhazanmu su zama mabarata a titunan Saudiyya saboda yankewar guzuri. kasahe da yawa wasu alhazan makonni biyu zuwa uku suke yi. Idan har aka tsara yadda jirgi zai gudanar da zirga-zirga, to za ka iya kwashe alhazanka kan lokaci.

Ya shawarci gwamnati da ta mayar da gudanr da harkar aikin Hajji ga kamfanoni masu zaman kansu. A cewarsa, hakan zai sa a samu aikin Hajii ingantacce, kasancewar za a samu gasa a tsakanin kamfanonin.

Ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki a tafiyar da aikin Hajji da su ji tsoron Allah, su sani cewa Alhaji bakon Allah ne; bai kmata ya zama abin cutarwa ba. Ya kuma shawarci hukumomin yaki da cin hanci na gwamanti da su binciki wannan al’amari tare da tilasta Hukumar NAHCON da ta dawo wa da alhazai ragowar kudaden da aka karba daga hannunsu, su kuma mutanen da aka samu da hannu a cikin wannan badakala, ya kamata su fuskanci hukunci don ya zama izna ga na baya.