A mayar da Hausa harshen kasa – Masana
Jami’ar Ahmadu Bello za ta shawo kan rikicin makiyaya da manoma Masana harsunan Afrika da suka halarci Babban Taron Duniya kan harshen Hausa da aka gudanar a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sun bukaci a fara amfani da harshen Hausa a matsayin harshen kasa a Najeriya, musamman ganin yadda ya samu karbuwa a sassan […]

Jami’ar Ahmadu Bello za ta shawo kan rikicin makiyaya da manoma
Masana harsunan Afrika da suka halarci Babban Taron Duniya kan harshen Hausa da aka gudanar a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sun bukaci a fara amfani da harshen Hausa a matsayin harshen kasa a Najeriya, musamman ganin yadda ya samu karbuwa a sassan kasar nan da Afirka da duniya baki daya.
Taron mai taken ‘kasar Hausa: Jiya da Yau da Gobe,’ Sashen Nazarin Al’adu Da Harsunan Afirka na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya ne ya shirya daga Talata zuwa jiya Alhamis.
Taron ya hado masana harsuna daga sassan duniya, inda suka ce bisa la’akari da yadda harshen ya samu karbuwa, lokaci ya yi da za a mai da shi ya zama harshen kasa, gwamnati ta rika gudanar da al’amuranta na yau da kullum da shi, kuma hakan zai taimaka wajen kawo hadin kan kasa da bunkasa tattalin arziki da saukaka al’amuran mulki da siyasa a kasar nan.
Shugaban taron, Mai shari’a Umaru Abdullahi, Walin Hausa ya kalubalanci masana harshen Hausa su maida hankali wajen gudanar da bincike ta yadda harshen zai kara bunkasa a daina ganin al’ummar Hausawa a matsayin cima-zaune, alhalin su ne suka gina kasar nan tare da tabbatar da hadin kanta, balle kuma yanzu da harshen ya bunkasa, ya buwaya a duniya.
A jawabin Shehun Malamin Hausa, Farfesa dandatti Abdulkadir, ya bayyana yadda harshen ya samu tagomashi a duniya inda manyan kasashe irin su Birtaniya da Amurka da Jamus da Faransa da China da sauransu ke amfani da shi wajen bunkasa mu’amalarsu da kasashen Afirka. Ya yi kira ga gwamnonin Arewa da sauran masu rike da madafun iko su hanzarta sanya harshen Hausa a matsayin harshen hukuma a Arewa, kuma a yi hobbasa domin ganin ya zama harshen kasa.
“Harshen Hausa ya bunkasa a duniya, yana daya daga cikin harsunan Afirka na sahun farko da gidan rediyon BBC ya fara amfani da shi wajen watsa labarai a duniya, kuma yana da miliyoyin masu saurare a duk fadin duniya. Harshen yana da duk abubuwan da ake bukata domin zama harshen kasa. Don haka, ya kamata ’yan siyasarmu, musamman gwamnonin Arewa su sanya ya zama harshen hukuma a duk fadin Arewa, sannan su yi kokarin ganin ya zama harshen kasa cikin gaggawa,” inji Farfesa dandatti.
Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Ibrahim Garba, ya bayyana bukatar a yi kokarin tabbatar da harshen Hausa ya zama harshen kasa, musamman saboda yadda ya bunkasa kuma ya mamaye ko’ina a Najeriya da nahiyar Afirka. Ya ce: “Mu a nan Jami’ar Ahmadu Bello, mun amince cewa harshen Hausa yana da kima da daraja, yadda ya karade ko’ina, musamman makwabtan kasashe da al’ummomin Afirka. Harshe ne na koyo da koyarwa kuma yana taimakawa wajen samar da hadin kai a tsakanin mabambantan al’umma.”
A jawabin, Shugaban Sashen Nazarin Al’adu da Harsunan Afirka na Jami’ar, Dokta Salisu Garba Kargi, ya ce sun shirya wannan gagarumin taro ne da nufin dada nuna wa al’ummar duniya matsayin da harshen Hausa ya kai. “Sanannen abu ne kuma tabbatacce cewa, bunkasar harshen Hausa da habakarsa a yau, ya isa ya zama harshen kasa, ta yadda za a rika gudanar da harkokin mulki da shi a Najeriya. Wannan ya sa aka shirya taron ranar Talata, 26 ga Nuwamba, 2016 domin kara tabbatar da matsayin harshen Hausa ba a Najeriya kawai ba, har da Nahiyar Afirka baki daya. Wancan taro ne ya bukaci lallai a kira babban taro na duniya, wanda zai game fannoni daban-daban don samar da cikakken bayani a kan al’ummar Hausawa da ire-iren albarkatun da suke jibge a cikin kasarsu,” inji Dokta Kargi.
Sauran masanan da suka gabatar da takardu kuma suka dada nuna inganci da buwayar harshen Hausa, sun hada da Farfesa Isma’ila Junaidu, Babban Sakataren Hukumar Tsara Manhajar Karatu ta kasa (NERDC) da ke Abuja da Farfesa Al-Amin Abu Manga, na Cibiyar Nazarin Al’amuran Afirka da Asiya a Jami’ar Khartoum da ke Sudan da Farfesa Nina Pawlak ta Cibiyar Nazarin kasashen Gabas da Sashen Harsuna da Al’adun Afirka ta Jami’ar Warsaw da ke Poland da Malam Abubakar Mahamman, Shugaban kungiyar Marubuta Harsunan kasa (ASSAUNIL) da ke Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Taron wanda aka kammala jiya Alhamis masana sun gabatar da takardun bincike sama da arba’in.