A mika Sherrif da Ihejirika ga Kotun Duniya – APC

Babbar jam’iyyar adawa a kasar nan Jam’iyyar APC, ta bukaci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya gaggauta mika wasu fitattaun ’yan kasar nan biyu tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Shariff da tsohon Babban Hafsan Sojojin kasar nan Janar Azubuike Ihejirika ga Kotun Hukunta Laifuffukan Yaki ta Duniya (ICC), domin su amsa tuhuma kan […]

A mika Sherrif da Ihejirika ga Kotun Duniya – APC
A mika Sherrif da Ihejirika ga Kotun Duniya – APC

Babbar jam’iyyar adawa a kasar nan Jam’iyyar APC, ta bukaci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya gaggauta mika wasu fitattaun ’yan kasar nan biyu tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Shariff da tsohon Babban Hafsan Sojojin kasar nan Janar Azubuike Ihejirika ga Kotun Hukunta Laifuffukan Yaki ta Duniya (ICC), domin su amsa tuhuma kan zarginsu da hannu a tallafa wa ayyukan kungiyar Boko Haram.
Jam’iyyar APC ta bukaci haka ne bayan zargin da wani mai shiga tsakani da Gwamnatin Tarayya ta gayyato daga kasar Autireliya Rabaran Stephen Dabis ya yi cewa tsohon Gwamnan Jihar Borno Ali Modu Sherif da tsohon Hafsan Hafsoshin Sojin Janar Azubuike Ihejirika na cikin masu tallafa wa kungiyar Boko Haram.
A wani taron manema labarai da Jam’iyyar APC ta kira a Abuja, ta ce dole ne Shugaba Jonathan ya mika mutanen biyu domin su fuskanci tuhuma kan zargin sa hannu a rikicin Boko Haram.
Sanata Ali Modu Sherriff wanda ake kira SAS an takaice kwanan nan ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC ya koma PDP.
Tuni dai mutanen biyu suka musanta zarge-zargen da ake yi musu na daukar nauyin Boko Haram.
Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Goodluck Jonathan da gaza magance matsalar Boko Haram a matsayinsa na Babban Kwamandan Askarawan kasar, inda ya bukaci ya tashi tsaye wajen magance matsalar dungurungum.
Gwamna Kwankwaso ya ce bai kamata a saka siyasa cikin lamarin ba a rika dora wa juna alhaki tsakanin bangaren gwamnati da na ’yan adawa ba.
Ya ce ’yan Boko Haram na kashe mutane ba tare da la’akari da addini ko siyasa ba, don haka ya kamata a hada hannu domin magance matsalar.
Sai dai bangaren Shugaban kasa ya musanta zargin da Gwamnan yayi kan cewar ya gaza magance rikicin. A cewarsa dakarun tsaron kasar na iyaka kokarinsu domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar nan.