‘A mike don kawar da gubacewar tarbiyya’

Shugaba al’ummar Arewa mazauna Abiele a Jihar Edo Alhaji Abubakar Sa’idu ya bukaci ’yan Arewa su tashi tsaye wajen hada kai da malaman addini da iyaye don koyar da tarbiyya tagari a  tsakanin matasa don ingatuwar addini da harkokin rayuwa. Alhaji Abubakar Sa’idu ya bayyana haka ne a zantawa da Aminiya a Abiele inda ya ce […]

‘A mike don kawar da gubacewar tarbiyya’
‘A mike don kawar da gubacewar tarbiyya’

Shugaba al’ummar Arewa mazauna Abiele a Jihar Edo Alhaji Abubakar Sa’idu ya bukaci ’yan Arewa su tashi tsaye wajen hada kai da malaman addini da iyaye don koyar da tarbiyya tagari a  tsakanin matasa don ingatuwar addini da harkokin rayuwa.
 Alhaji Abubakar Sa’idu ya bayyana haka ne a zantawa da Aminiya a Abiele inda ya ce ya kamata a ce daga wurin ’yan Arewa ne sauran al’ummar Najeriya za su koyi kyawawan halaye da nagartattun dabi’u da addini ya koyar game da harkokin rayuwa.
 Alhaji Sa’idu ya ce, “Wajibi ne shugabannin jama’a kuma ’yan Arewa da sauran shugabanni na Kudu da Gabas su himmatu a kan fadakar da jama’a da suke yi wa jagoranci kan muhimmancin zaman lafiya da neman ilimi, kuma su hada kai su kawar da gurbacewar tarbiyya da take yaduwa a tsakanin matasan kasar nan, domin ci gabanmu ya dore a samu zaman lafiya a kasar nan.”