A rage kudaden da ake ba shugabanni da ‘yan majalisar Najeriya

Ya zama dole a rarrage kudaden albashi da na alawus-alawus na duk wadansu zababbun ’yan siyasa tun daga kasa har sama. A nan ina nufin tun daga kansiloli har zuwa shugabannin kananan hukumomi, sannan da ’yan majalisar jihohi da majalisun gaba dayansu. Daga nan kuma sai a rarrage kudaden ’yan Majalisar Wakilai da ta Dattawa. […]

A rage kudaden da ake ba shugabanni da ‘yan majalisar Najeriya

Ya zama dole a rarrage kudaden albashi da na alawus-alawus na duk wadansu zababbun ’yan siyasa tun daga kasa har sama. A nan ina nufin tun daga kansiloli har zuwa shugabannin kananan hukumomi, sannan da ’yan majalisar jihohi da majalisun gaba dayansu.

Daga nan kuma sai a rarrage kudaden ’yan Majalisar Wakilai da ta Dattawa. Gaskiya kullum ana cewa talakawan kasa suna cikin matsin rayuwa amma an kasa ganin yaya al’amarin yake, kuma an yi mirsisi an ki fahimtar ababen da gangan da ganganci. Gaskiyar lamari gwamnati mai ci yanzu tunda ta kama ragamar mulki a shekarar 2015, sai kawai aka wayi gari ta kara kudaden albarkatun man fetur daga Naira 97 zuwa Naira 145 wanda karin ya shallake hankali kuma kananzir da gas duka aka yi musu karin da ya fi na arzikin Kundila.

To, ga masana sun ce an yi haka ne domin tafiyar da gwamnati mafi tsada, wato, ta launin yadda Amurka take yi “American System” to shi ne dalilin karin kudin man fetur da dangoginsa. Gaskiya, wannan akida ta gwamnati ita ta jawo tashin komai cikin Najeriya, ta janyo komai ya zama jangwam, kuma talakawa suka shiga cikin wahalolin rayuwa. Abu ne mawuyaci Gwamnatin Muhammadu Buhari ta juyo da baya domin gyara wannan kuskure tunda ’yan siyasar wannan zamani sun rungume ta ce domin lagwadar da ake samu ba wai domin kyautata wa jama’a ba.

Saboda haka, ya zama wajibi kowane dan majalisa ya saki rabin kudinsa domin taimaka wa kasa, haka Shugaban Kasa da ’yan majalisarsa da kuma dukkan ministoci. Haka ma gwamnoni da dukkan kwamishinoni da dukkan wanda aka nada a siyasance. Gaskiyar lamari, dole Shugaban Kasa ya yi iyakar iyawarsa domin ganin duk ’yan Majalisar Wakilai  da na Majalisar Dattawa duk wanda ya karbi aikin mazabu “Constituency Project” bai yi ba, lallai ya dawo wa gwamnati kudadenta.

Domin kuwa bai yi aikin ba, saboda haka ya zama dole ya amayar da kudaden da aka ba shi. Kuma daga karshe rokona ga Gwamnatin Tarayya shi ne a lura da iyakokin kasar nan, ba wai kawai a matsa kan shigo da motoci ba ko shinkafa, a’a shigowar baki ratata ba ya zame wa kasa abin alheri domin kashe-kashen bayin Allah sun yi yawa. Saboda haka, dole a hana shigowar bakin haure ta dukkan iyakokinmu duk da an ce daga na gida ake cin yakin gida.

Muhammadu Buhari a matsayinka na Shugaban Kasa da gwamnonin jihohi ku tashi tsaye domin ceto kasar nan kada ta wargaje, saboda son kai na wadansu mutane kalilan wadanda idan ba su samu mulki ba, sai dai Najeriya ta shiga halin ni-’yasu: Allah Ya tsare, amin.

Amma dai rage kudaden albashi da alawus-alawus na wadanda muka ambata zai zama alheri ga kasarmu Najeriya, sannan a rage kudaden man fetur da dangoginsa. Haka zai bada damar warware matsalolin Najeriya da jama’arta.

 

Kwamared Ibrahim Abdu Zango Kano. (08175472298 )