A rage yawan jihohi – Atiku Abubakar
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci a rage yawan jihohin kasar nan ta hanyar hade jihohin da ba su da katabus da masu katabus. Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake gabatar da laccar shekara-shekara ta Farfesa Ademola Popoola a Sashin Shari’a […]
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci a rage yawan jihohin kasar nan ta hanyar hade jihohin da ba su da katabus da masu katabus.
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake gabatar da laccar shekara-shekara ta Farfesa Ademola Popoola a Sashin Shari’a na Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile Ife, inda ya ce sake fasalin kasar nan zai kawo maslaha ta karshe kan matsalolin da suke addabar kasar nan.
Atiku wanda ya nuna damuwa kan yadda a koyaushe jihohi ke regegeniyar zuwa Abuja don karbo kason kudi, ya ce wadanda ba za su iya dogaro da kansu ba, rushe su.
Ya ce, “Babu shakka cewa jihohinmu da dama ba su iya katabus tun kirkiro su idan aka raba su da kason da suke samu daga Gwamnatin Tarayya a Abuja. Don haka wajibi ne mu samo hanyoyin da za su iya dogaro da kansu ta hanyar canja tsarin tarayya. Hadin kai a tsakanin jihohin da suke shiyya ko yanki daya zai taimaka.”
Alhaji Atiku Abubakar ya kara da cewa: “Za mu iya auna yiwuwar yin amfani da shiyyoyin siyasa da muke da su a matsayin tsarin sassan tarayya. Kuma za mu iya nemo wasu hanyoyi na yanke shawara kan inganci jihohi, misali ta hanyar bullo da wani tsarin gwaji da jiha za ta iya samar da wani kaso na kudin da take kashewa a cikin gida na wani ayyanannen lokaci da za a ajiye don tabbatar da tsayuwarta a kan kafafunta ko a hade ta da wata ko wasu jihohin.
Atiku ya ce sake fasalin tsarin tarayyar ba wata barazana ba ce ga hadin kan kasar nan ba.
Sannan kuma ya ce babu amfani Gwamnatin Tarayya ta mallaki Ma’aikatar Aikin Gona da ta Kiwon Lafiya, maimakon haka ta samu wasu sassa da za su rika sanya ido kan ma’aikatun, amma sai ga shi tana nada ministoci a kansu.
Alhaji Atiku Abubakar ya yi tambayar cewa: “Me ya hada Gwamnatin Tarayya da batun Ministan Ilimi ko Ministan Aikin Gona?”