A ranar Litinin Manchester United za ta fara yin balaguro

A ranar Litinin mai zuwa 13 ga watan nan da muke ciki ne ake sa ran kulob din Manchester United da ke Ingila zai fara yin balaguro a shirye-shiryen da yake yi na tunkarar kakar wasa mai zuwa. A wata sanarwar da kulob din ya fitar a ranar Litinin da ta wuce, ta nuna kulob […]

A ranar Litinin Manchester United za ta fara yin balaguro
A ranar Litinin Manchester United za ta fara yin balaguro

A ranar Litinin mai zuwa 13 ga watan nan da muke ciki ne ake sa ran kulob din Manchester United da ke Ingila zai fara yin balaguro a shirye-shiryen da yake yi na tunkarar kakar wasa mai zuwa.

A wata sanarwar da kulob din ya fitar a ranar Litinin da ta wuce, ta nuna kulob din zai kai ziyara Amurka ne inda zai fafata da kungiyoyin kwallon kafa daban-daban a wasannin sada zumunta a tsakanin ranakun 17 zuwa 29 ga watan.
Kulob din zai fafata ne a wasannin sada zumuntar da Amurka ke shiryawa a duk shekara a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa hudu ciki har da FC Barcelona na Sifen da kuma na PSG da ke Faransa.
United za ta hadu da kulob din Club America ne a ranar 17 ga watan nan a wasan farko yayin da a ranar 21 ga watan kuma za ta kece raini da kulob din San Jose Earthkuakes shi ma da ke Amurka. Sai ranar 25 ga watan ta hadu da kulob din FC Barcelona na Sifen kafin ta hadu da na PSG na Faransa a ranar 29 ga watan nan a wasanta na karshe a gasar.
A ranar Asabar 8 ga watan gobe (Agusta) ne ake sa ran za a fara gasar rukuni-rukuni na firimiya na Ingila, kuma United za ta fara wasanta na farko ne da kulob din Tottenham.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram