A ranar Litinin za a zabi Gwarzon dan kwallon Duniya
A ranar Litinin mai zuwa ne 12 ga watan nan da muke ciki za a sanar da Gwarzon dan kwallon Duniya a bikin da zai gudana a Hedkwatar Hukumar FIFA a Zurich da ke Swizilan. ’Yan kwallo uku ne za su fafata a gasar sun hada da Cristiano Ronaldo na kulob din Real Madrid kuma […]
A ranar Litinin mai zuwa ne 12 ga watan nan da muke ciki za a sanar da Gwarzon dan kwallon Duniya a bikin da zai gudana a Hedkwatar Hukumar FIFA a Zurich da ke Swizilan.
’Yan kwallo uku ne za su fafata a gasar sun hada da Cristiano Ronaldo na kulob din Real Madrid kuma haifaffen Fotugal da Lionel Messi, dan kwallon FC Barcelona na Sifen kuma dan asalin Ajantina da kuma Manuel Neuer, golan Jamus kuma yake buga wa kulob din Bayern Munich na Jamus kwallo.
Cristiano Ronaldo dai shi ke rike da kambun yayin da Lionel Messi ne ya taba lashe gasar sau hudu a jere yayin da Golan Jamus kuma bai taba lashe gasar ba.
Ana sa ran masu horar da kungiyoyin kwallon kafa daban-daban a sassan duniya da ’yan kwallo da ’yan jarida da kuma masana harkar kwallo ne za su kada kuri’unsu a yayin zaben.
Idan Ronaldo ya samu nasara, zai kasance ya lashe sau uku kenan yayin da idan Messi ya samu nasara zai kasance ya lashe sau biyar kenan. Idan kuma Manuel Neuer ne ya lashe, to wannan shi ne karonsa na farko.