A rayuwa: Ka yi kokarin sanin abokan gaba

Jama’a, ga gaisuwa nan kamar yadda muka saba a kowane mako: Assalalamu alaikum.Ga wata tambaya: A tsawon rayuwarka a wannan duniya, ko kana da abokan gaba? Haka ke ma ’yar uwa, kina da naki abokan gabar? Idan kana da su ko kina da su, wanda na tabbata ba za a rasa nono a riga ba, […]

A rayuwa: Ka yi kokarin sanin abokan gaba
A rayuwa: Ka yi kokarin sanin abokan gaba

Jama’a, ga gaisuwa nan kamar yadda muka saba a kowane mako: Assalalamu alaikum.
Ga wata tambaya: A tsawon rayuwarka a wannan duniya, ko kana da abokan gaba? Haka ke ma ’yar uwa, kina da naki abokan gabar? Idan kana da su ko kina da su, wanda na tabbata ba za a rasa nono a riga ba, to kin san su? Idan har kun amince kuna da abokan gaba kuma kun san su, to kun samu rabin maganin matsalarku ta wannan fuska, sai ku yi kokarin neman rabin maganin, wanda shi za mu ba ku a wannan maudu’in. Idan kuwa har ba ka san abokan gabar ka ba, to lallai ne ka fara bincike, domin ka gano wanda ko wacce ke ganin kyashin nasarar da kake samu a rayuwa, wanda shi ne ko ita ce abokar gaba a gare ki.
A rayuwa, abu ne mai sauki mutum ya gane mai kaunarsa ko mai son shi, domin kuwa soyayya ko kauna wasu abubuwa ne da tasirinsu kan fita karara kuma cikin lokaci. Alhali gaba ko kiyayya wata abu ce mai wuyar sha’ani, wacce ba kasafai mutum kan fito karara ya nuna wa dan uwansa ba. Wani lokacin a munafunce akan nuna haka kuma ba kai tsaye ba. Wannan dalili ya sanya sai ka ga an dauki tsawon lokaci kafin tasirin kiyayya ya bayyana karara ga mutum. Hakan ya sanya sai ka dade da mutum, yana kin ka ko yana gaba da kai, amma baka sani ba. Idan ma ba a yi sannu ba, mutum na iya daukar abokin gabarsa a matsayin masoyinsa. Don haka, lallai abu ne mai kyau a rayuwa, mutum ya yi kokarin gano wadanda ke gaba da shi. Bayan ka gano abokin gaba, kada ka tsaya nan, ka yi kokarin yin bincike, domin sanin dalilin da ya sanya wannan mutum ke gaba da kai.
Kafin mu ci gaba da wannan bayani, bari mu amsa wata tambaya. Shin me ake nufi da abokin gaba? Abokin gaba shi ne wani mutum, mace ko namiji da a kullum yake hassada da bakin ciki da kai. Mutumin nan, mace ko namiji, ba ya son ganin ka samu natsuwa da farin ciki a rayuwa. Ba ya son ya ga ka samu nasara a wajen aikinka ko kuma wajen sana’arka. Irin wadannan mutane, su ne ba su kaunarka ta kowace fuska. Idan sun ga kana dariya, suna jin  kamar ana sukar su ne da konannen tsinin mashi. Idan kuwa wani dalili ya sanya suka ga kana kuka ko kana cikin wani takaici, to a lokacin ne suke farin ciki da annashuwa, suna jin kamar an nada su sarautar Santanbul. Idan har akwai irin wadannan mutanen a cikin rayuwarka, babu shakka, babu tantama, su ne abokan gabarka.
A ina ake samun irin wadannan abokan gaba? Ana samun su a ko’ina cikin al’umma. Wasu ma abokanka ne, wadanda kuka taso tun daga kuruciya, wasu kuwa kana haduwa da su ne a wajen aikinka ko kuma wajen sana’arka. Haka kuma ana samun abokan gaba a dalilin makwabtaka, a gida ko a dalilin shiga mota ko a makaranta ko ta makabtaka a wajen aiki. Haka kuma ana samun abokan gaba daga cikin dangi na jini, ya Allah ’yan uba ko kuma ma tsakanin wa da kane ko ya da kanwa, wadanda suka fito ciki daya, uwa daya uba daya. Na san kila ka yi mamaki. Babu mamaki, tabbas tana faruwa. Domin tarihi ya nuna mana yadda gaba ta farko ta faro a duniya, tsakanin ’ya’yan Annabi Adamu (AS), wato Habila da kabila. Ana samun abokan gaba tsakanin magidanta ko tsakanin kishiya da kishiya da sauransu. Haka kuma, ana samun gaba tsakanin miji da mata. Miji da mata su rika yin gaba da juna, duk da cewa sun yi aure na soyayya? kwarai kuwa, kada ka raba daya biyu, ana samu miji da mata su rika gaba da juna, domin rayuwar nan ta duniya shu’uma ce!
Za mu ci gaba makon gobe in Allah Ya kai mu