A rayuwa: Ka yi kokarin sanin abokan gaba (2)

A ina ake samun irin wadannan abokan gaba? Ana samun su a ko’ina cikin al’umma. Wasu ma abokanka ne, wadanda kuka taso tun daga kuruciya, wasu kuwa kana haduwa da su ne a wajen aikinka ko kuma wajen sana’arka. Haka kuma ana samun abokan gaba a dalilin makwabtaka, a gida ko a dalilin shiga mota […]

A rayuwa: Ka yi kokarin sanin abokan gaba (2)
A rayuwa: Ka yi kokarin sanin abokan gaba (2)

A ina ake samun irin wadannan abokan gaba? Ana samun su a ko’ina cikin al’umma. Wasu ma abokanka ne, wadanda kuka taso tun daga kuruciya, wasu kuwa kana haduwa da su ne a wajen aikinka ko kuma wajen sana’arka. Haka kuma ana samun abokan gaba a dalilin makwabtaka, a gida ko a dalilin shiga mota ko a makaranta ko ta makabtaka a wajen aiki. Haka kuma ana samun abokan gaba daga cikin dangi na jini, ya Allah ’yan uba ko kuma ma tsakanin wa da kane ko ya da kanwa, wadanda suka fito ciki daya, uwa daya uba daya. Na san kila ka yi mamaki. Babu mamaki, tabbas tana faruwa. Domin tarihi ya nuna mana yadda gaba ta farko ta faro a duniya, tsakanin ’ya’yan Annabi Adamu (AS), wato Habila da kabila. Ana samun abokan gaba tsakanin magidanta ko tsakanin kishiya da kishiya da sauransu. Haka kuma, ana samun gaba tsakanin miji da mata. Miji da mata su rika yin gaba da juna, duk da cewa sun yi aure na soyayya? kwarai kuwa, kada ka raba daya biyu, ana samu miji da mata su rika gaba da juna, domin rayuwar nan ta duniya shu’uma ce!
Har yanzu dai ina kara jawo hankalinmu ga maudu’inmu na yau, mu yi kokari mu gano ko mu san abokan gabarmu a rayuwa. Amma ta yaya za mu gano su, kuma idan mun gano su, me ya kamata mu yi a kansu? Ma’ana, idan na gano wane ko wance abokin gaba ne a gare ni, wane mataki ya kamata in dauka a kansa ko a kanta? Darasin maudu’inmu na yau ke nan, kuma za mu warware shi da ikon Allah.
Idan ka gano wane ko wance abokin gaba ne a gare ka, babban abin da za ka yi shi ne, sai kuma ka yi kokari ka gano dalilin da ya sanya yake gaba da kai. Idan ka gano dalilin nan shi ne kuma makami ko maganin da za ka yi amfani da shi wajen magance wannan gaba da yake ko take yi da kai. Domin kuwa duk wani ko wata da zai tsiri gaba da wani, sai yana da wani dalili na musamman. To wannan dalilin, shi za ka gano sannan kuma shi ne Panadol da za ka hadiya domin ya magance maka wannan gaba.
Misali, wani zai yi gaba da kai ne saboda kawai ka fi shi dukiya ko ka fi shi sututra. Sai kawai ya ji ya tsane ka, ya ji bai son ka. Me ya kamata ka yi a wannan gaba? Tun da dai ka gano cewa yana gaba da kai ne saboda abin duniya, wanda kai Allah Ya ba ka, sai ka yi kokarin kyautata masa, ka rika yi masa kyauta da abin nan da Allah Ya ba ka. Na tabbata ba zai ci gaba da gaba da kai ba, maimakon haka ma, zai dawo yana kaunarka. Don haka, yi kokari ka gano abokin gabarka, sannan ka fahimci dalilin da yake gaba da kai, sai ka magance gabar da wannan.
Amma kuma akwai wani ko wata da za su rika gaba da kai haka kawai, saboda kawai hassada da bakin ciki. Irin wadannan mutane, babu abin da za ka yi ka dadada musu bare har ka magance wannan hassada tasu. Idan haka ta faru, tun da dai ka gano cewa suna gaba da kai ne kawai domin kyashi da hassada, to sai ka jajirce, ka ci gaba da neman wannan abu da suke maka hassda a kansa. A sakamakon wannan kokari naka na nema, Allah zai ci gaba da ba ka nasara. Wannan nasara da kake samu a kullum, ita ce maganin gabar da wane ko wance suke yi maka. Ke nan, a lokacin da kake kara samun nasara, su kuma suna kara samun kunar zuciya da rashin sukuni. Ka yi maganinsu ke nan.
Wani muhimmin abu da ya kamata mu kara fahimta da wannan misali da muka yi a sama shi ne, idan mun gane wane ko wance abokan gaba ne a gare mu, kada mu ce za mu biye musu mu rika gaba da su. A’a, kada ma mu yi musu mugunta ko mu tadiye musu kafa. Wannan ba shi ne maganin ba, domin duk mai hankali ba ya rama mugunta da mugunta. A lokacin da ka bata lokacinka wajen yin mugunta ga abokin gabar ka, za ku yi abin da ake kira ragas, ko kuma kamar yadda Hausawa suke cewa, za ku yi mutuwar kasko. Ba wannan ne abin bukata ba.
Kamar yadda wani mai hikima ya taba ambatawa, ya ce: “Kada ka bata ingantaccen lokacinka domin ka burge abokin gabar ka. Maimakon haka, ka kara himma da kwazo wajen ganin ka cimma nasara kan abin da yake gaba da kai ta dalilinsa, ta yadda a kullum zai ga kana ta samun nasarar a wannan fage.”
Allah Ya sanya mu gane makiyanmu kuma Ya ba mu ikon murkushe kiyayyarsu daga gare mu, amin. Sai kuma makon gobe idan Allah Ya kai mu, inda za mu lalabo wani sabon maudu’in na Sinadarin Rayuwa.