A rayuwa, ko ka san inda ka sa gaba kuwa? 1
Ga masu bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, ina yi maku sallama, kamar yadda muka saba: Assalamu alaikum. Bayan haka, a wannan makon kuma, za mu yi ninkaya ne a cikin sabon maudu’i, kamar yadda muka nuna a sama.Kafin mu shiga tsokacin namu kai tsaye, mu fara da wani takaitaccen labari, wanda shi ne zai […]
Ga masu bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, ina yi maku sallama, kamar yadda muka saba: Assalamu alaikum. Bayan haka, a wannan makon kuma, za mu yi ninkaya ne a cikin sabon maudu’i, kamar yadda muka nuna a sama.
Kafin mu shiga tsokacin namu kai tsaye, mu fara da wani takaitaccen labari, wanda shi ne zai share mana hanya, domin fahimtar jigon madu’in namu.
Wani manomi ne da ya mallaki wani kare mai karsashi da kazar-kazar. Karen nan ba ya zama ko’ina sai bakin titi kuma halinsa ne a duk lokacin da mota ta zo wucewa a hanyar, sai ya rika bin bayanta da gudun tsiya da nufin sai ya wuce ta. Haka yake yi a kowane lokaci, tare da haushi mai karar tsiya.
Kan haka ne sai makwabcin manomin nan ya yi masa tambaya: “Malam, wai shi karen nan naka, kana ganin akwai ranar da zai iya cin ma mota a wurin gudu kuwa?”
Jin haka sai manomin nan ya amsa masa da cewa: “Ni ba ma abin da ke damuna ba ke nan. Ni abin da nake tunani kuma yake damuna shi ne, idan ma har ya yi nasarar cin mata, to me zai yi kuma? Me zai samu da zai amfane shi, idan ya kamo motar da yake bi ko kuma idan ya tsere mata?”
Wannan shi ne labarin manomi da karensa da kuma tambayar da makwabcinsa ya yi masa. Idan mun nazarci labarin nan a tsanake, za mu iya ganin darussa masu kyau da za mu iya koya a rayuwarmu ta yau da kullum. A rayuwarmu ta yau da kullum, akwai mutanen da suka yi kama da karen manomin nan, wadanda ke gudanar da rayuwarsu ba tare da sanin hakikanin inda suka sa gaba ba. Ma’ana, kamar yadda karen nan yake bin motoci da niyyar sai ya wuce su ko kuma sai ya kamo su, alhali babu wani abin da zai amfana daga haka, to haka ma wasu mutane ke yin wasu ayyuka na babu-gaira-babu dalili, ayyukan da ba za su amfane su ba a rayuwa. Ta haka za ka ga sun dauki wata hanya, wacce ba su ma san dalilin daukar ta ba, haka kuma ba su san ma inda suka nufa ba a rayuwa. Yin haka kuwa ba karamar asara ba ce, domin kuwa ga duk mai yin haka, babu abin da zai samu sai faduwa da asara.
Bari mu sake bibiyar maudu’in nan namu da misalai na zahiri, domin mu kara fahimtar abin da yake koyar da mu. dauki misalin dan makaranta, wanda a kullum ake bukatar ya rika zuwa makaranta domin daukar darasi. Shin me ya kamace shi ya yi? Kamata ya yi ya fahimta da cewa ya sa gabansa ne wajen neman ilimi. Ilimin da zai samu kuma zai zame masa mai amfani a duk tsawon rayuwarsa. Idan dalibin nan ya fahimta da cewa lallai ga inda ya sa gaba, to wannan za ta ba shi damar ya maida hankali ga zuwa makaranta a kan lokaci, ba fashi. Sannan kuma zai ba da kokari wajen yin karatu da nazari, domin ya samu nasarar cin jarabawa.
A daya bangaren kuma, idan dalibin nan ya zabi ya yi koyi da rayuwar karen manomin nan, to sai ya yi watsi da makaranta. A makwafinta sai ya dauki wani aiki marar tasiri da muhimmanci, ya rika gudanarwa. Misali, yana iya daukar tadar nan ta kallon kwallon Turawa. Kullum shi ne bata lokaci wajen kallo, dare da rana. Shi ne karance-karancen labarinsu da kokarin sanin abin da suke ciki. Za ka ga ya haddace sunayen ’yan kwallo na kungiyoyi da yawa, ya san yawan kudin da suke samu, ya san kudin da wata kungiya ta zuba, ta sayi dan wasa kaza, da sauransu. Ta haka dai za ka ga dukkan al’amuransa sun ta’allaka ga al’amuran wannan kwallo.
Idan zan tambaye ka, a matsayin wannan matashi na dalibin makaranta, me kallon kwallon Turawa zai tsinana masa? Ashe wannan aiki da ya tanadar wa kansa bai yi daidai da aikin da karen manomi ya diba wa kansa na bin mota ba? Yadda karen nan ba zai amfana da komai ba, haka shi ma dalibin nan ba zai samu komai ba a rayuwarsa. Iyaka abin da zai samu shi ne, dala miliyan kaza Rooney ke samu, kungiya kaza ta sayi Ronaldo kan dala miliyan kaza… illa iyaka.
Don haka, kada mu yi koyi da aikin karen manomi, mu rika yin aikin da zai amfane mu a rayuwa. Mu tabbatar mun san alkiblar da muka dosa tun kafin mu fara tafiya. Ta haka ne za mu samu nasarar al’amuranmu na rayuwa, domin kuwa ta haka ne za mu kauce wa abin nan da Hausawa ke kira ‘zuwan kare a karofi, ba rini ba matsa.’ Alla Ya taimake mu, amin.