A Rayuwa: Mu fahimci mutum domin fahimtar mu’amala da shi
Ya ku ma’abuta bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, ina yi maku gaisuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, yau kuma muna dauke da sabon maudu’i, wanda ya danganci hanyoyin da za mu fahimci yanayi da halayen mutane, wanda haka zai ba mu damar fahimtar hanyoyin da za mu bi da kowane mutum da Allah Ya hada […]
Ya ku ma’abuta bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, ina yi maku gaisuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, yau kuma muna dauke da sabon maudu’i, wanda ya danganci hanyoyin da za mu fahimci yanayi da halayen mutane, wanda haka zai ba mu damar fahimtar hanyoyin da za mu bi da kowane mutum da Allah Ya hada mu mu’amala tare da shi.
Kowane mutum yana tafiyar da rayuwarsa ce daidai da tunaninsa, daidai da abin da ya koya, ya siffatu da shi. Tunanin kowane mutum yana tasirantuwa ne da wurin da yake zaune, da irin mutanen da ya taso cikinsu, sannan kuma yakan fitar da ayyukansa ne daidai da abin da yake adane a zuciyarsa ko rayuwarsa.
Idan mutum ya taso cikin masu ilimi da aiki da shi, babu shakka zai tasirantu da ilimin nan, sannan kuma mu’amalarsa da yadda zai tafiyar da rayuwarsa cikin mutane, za su kasance ne bisa ilimin nan da ya kimshe a kirjinsa.
Idan mutum ya kasance cikin mutane masu kyakkyawar tarbiyya, babu shakka zai koyi wannan dabi’a kuma hakan zai yi masa tasiri a wajen mu’amalarsa da al’umma. Haka kuma abin yake ga wanda ya taso cikin al’umma masu gurbatattar tarbiyya, abin da zai yi tasiri ga rayuwarsa ke nan.
dabi’a ce ta rayuwa, dan Adam yana aiwatar da wani abu ne da ya siffantu da shi. A misali, mutum yanayin aiki ne ko kuma yana yin kyauta ne da abin da yake da shi. Don haka mutum ba zai iya kyauta da abin da bai da shi ba. A duk lokacin da ka ga wani ya yi maka kyauta ko ya aikata maka wani abu, to iya abin da ya mallaka ke nan ko kuma iya abin day a koya ken an kuma ya kasance tarbiyyarsa. Ga misali:
A lokacin da mutum ya yi maka kyauta ta kudi, tabbas ya mallaki kudi. Bai yi maka kyautar nan ba, sai da ya tanadi ko ya mallaki abin da ya ya yi maka kyauta da shi. Haka kuma, sai da ya samu ilimi da tarbiyyar yin kyauta, sannan ya yi kyautar. Idan da rowa ya koya, to tabbas abin da zai yi maka ke nan, domin ya mallaki tarbiyyar rowa, don haka ita zai raba ga abokan mu’amalarsa.
A lokacin da mutum ya nuna maka kyakkyawar mu’amala, babu shakka ya mallaki dabi’ar kirki kuma ya koya ne daga al’ummar da ya taso ya rayu cikinta. Da ya mallaki akasin wannan tarbiyya, da babu yadda za a yi ya aiwatar da mu’amalar kirki, domin bai tasirantu da ita ba. Tun da kuwa bai mallaki tarbiyyar kirki ba, yaya zai fitar da abin kirki daga jikinsa ko tarbiyyarsa?
A lokacin da mutum ya kunduma maka zagi ko ya yi maka sharri, babu shakka ya kasance ya mallaki dabi’ar banza. Kuma babu yadda za a yi ka canja shi daga wannan turba, domin abin da ya sani ke nan kuma ya mallaka a matsayin dabi’a.
A lokacin da mutum ya yi maka butulci, babu shakka shi ya kasance wanda ya siffatu da tarbiyyar butulci. Don haka, idan a rayuwa ka gamu da mai wannan dabi’a kuma ya yi maka, to kada ka yi mamaki kuma kada ka ce za ka dagula wa kanka lissafi, domin kuwa tun ran gini, tun ran zane. Iyaka abin da ya mallaka ke nan, tarbiyyar butulci, kuma mutum na aiwatar da abin da ya tarbiyyantu da shi ne. Yaushe asharari zai yi halin kwarai? Yaushe mai tarbiyya zai yi halin asharari? Ke nan kowa da kiwon da ya amshe shi, ko kuma mu ce, kowa da sandar da ke hannunsa yake jifa.
A lokacin da mu’amala ta hada ka da mutum, za ka iya fahimtarsa ne ta aikinsa ko ta kalamansa da ya yi a gare ka. Maha’inci, halayyarsa na bayyana ne idan ya yi ha’inci gare ka. Mai gaskiya, garkiyarsa na bayyana ne a lokacin da ya yi maka aikin gaskiya. Butulu yana bayyana ne a lokacin da ya aikata maka butulci a yayin mu’amalarku.
Idan ka fahimci mutum, za ka iya zama da shi da halinsa. Har kullum dai abin da ya kamata shi ne, ka yi kokarin bambance fari daga baki, ka bambance mai kyau daga akasinsa, ka bambance aikin kwarai daga gurbatacce. Ka yi kokari iya yinka ka zauna da mutanen kwarai domin ka kasance nagartacce. Ka kasance mai lizimtar alheri, domin ka kauce wa mugu da mugunta.
Saboda wadannan dalilai na sama, me ya kamata ka yi, a lokacin da ka samu wani ya yi maka ba daidai ba a yayin mu’amala? Kai ka kasance mai alheri, mai karimci kuma mai albarka ga al’umma. Kada ka mayar da mugunta da mugunta, kada ka maida butulci da butulci, kada ka mayar da zagi da zagi. Wanda ya yi maka rowa, idan ka samu damar yi masa alheri, ka yi masa. Wanda ya zage ka, ka yi masa addu’ar alheri. Idan ka yi haka, ka zama mai alheri kuma ka zama mai arzikin duniya da lahira.
Ya Allah Ka sanya mu masu rabon alherinKa duniya da lahira. Amin.