A rayuwa: Mu san hikimar zama da mutum
“dan Audu mutum mugun icce/Shi za ka dasa nai sai yai girma/Kuma yai inuwa tai luf-luf-luf/In ka so shan inuwar ku yi tawaye!” – Marigayi Mamman Shata KatsinaKamar dai yadda muka saba, yau ma Allah Ya sake hada mu a cikin wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Ina yi muku sallama da gaisawa kamar kullum, Assalamu […]
“dan Audu mutum mugun icce/Shi za ka dasa nai sai yai girma/Kuma yai inuwa tai luf-luf-luf/In ka so shan inuwar ku yi tawaye!” – Marigayi Mamman Shata Katsina
Kamar dai yadda muka saba, yau ma Allah Ya sake hada mu a cikin wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Ina yi muku sallama da gaisawa kamar kullum, Assalamu alaikum.
Kada ku yi mamakin yadda na bude maudu’in wannan makon da tsakure daga wakar marigayi Dokta Mamman Shata Katsina, ba don komai ya sanya na yi haka ba, sai saboda dacewar wannan waka da abin da za mu tattauna a yau; wato halayen mutum tare da jawo hankalinmu domin mu yi taka-tsan-tsan da halayensa.
Babu ko shakka, mutum dan Adam jikan mutuwa, wata halitta ce mai wuyar sha’ani, mai wuyar fahimta. Kuma ga shi a rayuwar yau da kullum da muke a doron kasa, shi mutum ne shugaban dukkan halittu, kuma ga shi ya zama dole kuma wajibi mu rayu tare da mutum. Abin tambaya shi ne, to ta yaya za mu jure zama da mutum a matsayinmu na mutane? Amsar guda daya ce, dole ne mu yi taka-tsan-tsan da mutum da halayensa.
Ita dai rayuwar nan ’yar lura ce, kuma ’yar a bi a sannu a hankali ce. Ba ta bukatar garaje, duk abin da za ka yi, ka tsaya sannu a hankali ka nazarce shi, kafin ka saka kanka ciki. Duk mutumin da Allah Ya hada ka zama da shi, ya Allah makwabtaka ce ko kuma ta bangaren sana’a ko aiki, ko kuwa ma a hanya kuna tafiya tare kuka hadu, ya zama wajibi ka yi nazarin halayensa domin ka fahimce shi, sannan ka san yadda za ka zauna da shi. Domin kuwa muddin ka ce za ka rika yin mu’amala da mutane ido rufe, ba tare da nazari ba, to yanzu-yanzu ka sha mamaki. Domin kuwa shi mutum, kamar yadda na ambata a baya, halitta ne mai wuyar sha’ani, wanda ke bukatar kyakkyawan nazari domin fuskantar mu’ala mai fa’ida da shi.
Kafin sannan, mataki guda ya kamata ka dauka game da kowane irin mutum Allah Ya hada ka da shi. Kai dai ka kasance kaifi daya, mai budaddar zuciya guda tsakaninka da kowane mutum. Tsaninka na mu’amala ya kasance gaskiya da gaskiya. Abin da duk ka san za ka iya, to ka yi shi daidai iyawarka, abin da kuma ka tabbata ya fi karfinka, to ka tsaya nan, kada ka ce za ka yi abu don gwaninta ko don nuna isa. Ta haka ne za ka iya cin ribar zama da mutum cikin fa’ida.
Ya kamata ka san cewa, idan ka ce za ka yi mu’amala da mutum bisa wata manufa ta daban, wacce ba bisa turbar gaskiya da budaddar zuciya ba, to babu yadda za ka iya burge mutum. Wata rana sai ya ba ka ruwa, ke nan idan ka yi mu’amala da shi don nunawa, ko don burge shi, wanda haka ya sanya ka tarbi abin da ya fi karfinka, to ka sani cewa da zarar abin ya ba ka ruwa, to ba ka da kaico. Amma idan bisa kaifi daya ka yi mu’amalar da shi, bisa gaskiya-da-gaskiya, to ko da daga baya ya yi maka butulci, abin ba zai dame ka ba, ba zai dagula maka lissafi ba, domin kuwa ka riga ka ci maganin haka, tun da bisa gaskiya ka tsaya. Domin kuwa masu salon magana na cewa, ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi.
Wani abu kuma da ya kamata ka yi tsakaninka da mutum shi ne, kada ka sake ka rama mugunta da mugunta, domin kuwa ita mugunta fitasrin fako ce, mai ita take koma mawa komai daren dadewa. Don haka idan ka sake ka rama mugunta da wata muguntar, to kai ma taka za ta dawo maka. A nan gara ka yi hakuri da duk abin da ya same ka na daga muguntar da wani ya kulla maka, domin kuwa za ta wuce, kuma daga karshe ka zama cikin kubuce mata da yardar Mai Duka.
Ya kamata ka gane cewa kowane mutum na dauke da halaye biyu ne, baki da fari. Inda labarin ke canzawa shi ne, idan halayen mutum bakake suka rinjayi farare, sai ka same shi tantagaryar mugu dan muguwa. Shi ne za ka ji yawan mutane na kuka da shi, ana yin Allah wadarai da halayensa. Mutum irin wannan ne ke zama bara-gurbi, mai aikata muggan ayyuka na cutar jama’a. Ka samu irin wannan mutum da aikata kisan gilla, cuta, zamba cikin aminici da sauran muggan alkaba’i da mutum irinsa kan iya aikatawa. Irin wannan mutum ne ke zama abin kyama da gudu ga jama’a.
Amma idan aka yi sa’a, halayen mutum suka kasance farare, suka zama sun rinjayi bakaken, to nan ne za ka ga mutumin kirki, mai kyawawan halaye, abin sha’awa ga kowa. Shi ne za ka ji ana kira da Allah-san-barka. Shi ne wanda za ka gani ko ka ji ana labarin cewa mutumin kirki ne, mai halayen kirki, wanda kowa ke son mu’amala da shi. Irin wannan mutum ne wanda za ka ji shi da aikata ayyukan alheri, shi ne kyauta da sanin ya kamata, da taimakon al’umma ta hanyar aikinsa ko sana’arsa, shi ne mai zumunci da ’yan uwa da abokan arziki. Shi ne mai sauki da saukakawa ga al’umma.
Tun da mun gane haka, to ga wani kalubale: Cikin irin wadannan mutane, wanne kake son a danganta ka da shi? Mugun mutum ko kuwa na kirki? Na tabbata ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, kana son ka ji an ce kai na kirki ne, ba za ka so ma ka ji an ce kai na banza ba ne ko mugu ba. Idan haka ne, me zai hana mu kasance na kirki a zuci da aikace? Wannan ce kawai babbar hanyar da za mu tsira a nan duniya da lahira! Sai mun hadu a mako mai zuwa in Allah Ya yarda.