A rayuwa: Mu zabi abokanen kirki

Masu karatu, Assalamu alaikum. A wannan makon kuma za mu duba wani sabon maudu’in ne na daban. Wato bayani game da halayyar zama da abokai da kawaye.A rayuwa, dan Adam ba zai iya zama shi kadai ba. Idan ma har ya amince ya zauna shi kadai din, to ba haka aka so ba, wai kanen […]

A rayuwa: Mu zabi abokanen kirki
A rayuwa: Mu zabi abokanen kirki

Masu karatu, Assalamu alaikum. A wannan makon kuma za mu duba wani sabon maudu’in ne na daban. Wato bayani game da halayyar zama da abokai da kawaye.
A rayuwa, dan Adam ba zai iya zama shi kadai ba. Idan ma har ya amince ya zauna shi kadai din, to ba haka aka so ba, wai kanen miji ya fi miji kyau. Mutum zai iya zama shi kadai ne kawai bisa lalura, wacce ba zai iya maganinta ba. Dalili ke nan ya sanya za ka ga mutane na zaune cikin gidaje, a unguwanni, a garuruwa da kasashe daban-daban. Haka kuma ta sanya za ka samu kowane mutum na da abokai, idan mace ce kuwa, tana da kawaye ke nan. To, wajen zabe da zama da abokai da kawaye, nan ma akwai abin lura da kula sosai, domin kuwa shi zaben da kuma zaman, wani yanayi ne na rayuwa na musamman. Don haka yana bukatar a zizara masa sinadari shi ma, domin a samu fa’idar rayuwa, domin a samu rayuwa cikin dacewa da amfani.
Masu iya magana sun ce, abokin damo guza, kamar kuma yadda suka ce, abokin barayo barawo ne. Abin da wadannan karin maganganu ke nufi a fili yake, musamman idan mun danganta shi da halayyar dan Adam ta fuskar rayuwar yau da kullum.
Shi mutum, kamar yadda muka dan yi bayani a sama, ba zai iya zama shi kadai ba, wannan halayya ce ta sanya kuma ya kasance mai kwaikwayo. A halayya da dabi’a, mutum ya kasance mai kwaikwayo, mai rikida kamar hawainiya. Duk inda ya samu kansa, muddin ya ladabtu da yanayin wurin, to wannan ne zai kasance halayyarsa ta rayuwa. Ke nan duk yanayin irin abokan zamansa ko abokan mu’amalarsa, to irin wannan halayya zai kwaikwaya kuma ta zama dabi’a da al’adar rayuwarsa
Abin bukata a nan shi ne, mutum ya iya zaben abokin zamansa, wanda zai dace da yanayi da rayuwa mai fa’ida ba gurbatatta ba. Yin haka wani sinadari ne shi ma a rayuwa. Musamman ma idan muka dauki ma’anonin wadannan karin maganganu da muka kawo misalinsu a sama.
To, ta yaya mutum zai zabi abokin rayuwa ko kawa? Abin sauki gare shi a wani bangaren, ta wani bangaren kuma, ba abu ne mai sauki ba. Sai dai duk yadda ta kasance, bari mu dan ba da wata ’yar shawara, ko za mu iya samun mafita idan muka bi ta.
Kafin ka yi abokantaka da mutum, ya kamata ka san ko shi wane ne? Yaya halayensa suke? Ko yana da kamala da mutunci a cikin mutane da bayansu? Ko shi mutum ne mai gaskiya da rikon Amana? Ko shi muzakkari ne mai himma da kwazo da kokarin neman halaliyarsa? Shi ba raggo ba ne, malalaci mai son jikinsa? Shin wannan mutum da ka ke son abokantaka da shi, ko yana son addini da aikata hukunce-hukuncensa? Yana da kishin kasa da kishin kansa da kishin al’ummarsa? Muddin dai amsoshin da ka samu daga wadannan tambayoyi sun kasance haka mutumin yake, to babu shakka idan ka yi abokantaka da shi ba za ka yi da na sani ba. Domin kuwa tabbas kai ma yau da kullum za ka kasance kamarsa, mai irin halaye kamar nasa.
Kamar ke kuwa ’yar uwa, ke ma ya dace ki lura da wasu abubuwa, kafin ki kulla kawance da wata abuya. Ya dace ki lura da halayenta sosai, idan ba haka ba kuwa, to kila ki yi da na sanin kawance da ita. Ya dace ki gane yanayin halaye da dabi’un kawarki. Shin ita ba asharariya ba ce? Ita ba gantalalla ba ce? Tana jin maganar magabatanta? Tana da kunya da kamala? Mai irin wadannan halayen, ita ce za ta zame maki kawa mai fa’ida, wacce za ku amfani juna a rayuwarku.
Abin da duk wannan ke nuna mana shi ne, yanayin abokinka ko kawarki, to yanayinka ko nata ke nan. Idan kina kawance da karuwa, babu shakka ko da ba ki karuwanci, to sunanki karuwa a idanuwan jama’a. idan kana abokantaka da barawo, babu shakka kai ma barawo ne, ko da kuwa ba ka yin sata. Kuma sannu a hankali, kai ma sai ka zama barawon wata rana.
Haka kuma, akwai wata azancin magana da ke cewa, ka nemi abokin zama tun kafin ka samu wurin zama. Domin abokin zama na kwarai shi ya fi wahalar samu fiye da wurin zaman. Duk dai azancin wannan ya tsaya ne wajen yin taka-tsan-tsan wajen neman abokin zama. Duk mutumin da ya siffatu da zama tare da malami, to da sannu zai zama malami shi ma, domin yau da kullum ba ta bar komai ba. Kasancewar yana tare da malamin nan, dole ne ya rika koyon ilimi, musamman domin halayya ta dace. Kasancewar masu iya magana suna cewa, sai hali ya yi daidai sannan ake abokantaka.
Ke nan ya dace mu tsarkake zukatanmu, mu kyautata halaye da dabi’unmu, mu kasance tare da abokai da kawaye na kwarai, masu mutunci da kamala. Ta haka mu ma za mu zama masu ktyawawan halaye, masu kyautata al’amuran rayuwarmu. Haka zai sanya a samu al’umma mai mutunci ba gurbatatta ba, wanda haka ne zai tabbatar da ci gaban kasa da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.  
Wannan a bayyana yake, domin idan mutane suka kasance masu halayen kirki saboda suna tare da abokai da kawayen kirki, to waye zai zama na banza mai halin banza a cikin su? Ni kuwa na ce da wuya a dafa kaza, sannan a yar da ita. Don haka mu kula sosai da halayen rayuwa, musamman ta hanyar zaben abokai da kawayen da suka kamata mu zauna tare da su cikin zumunci da hulda. Sai kuma mun hadu a mako na gaba.