A rika ba bangaren kiwon lafiya fifiko a kasafin kudi – Hajiya A’ishatu
Shugabar sashen kula da lafiya a matakin farko ta karamar Hukumar Dawakin Tofa, Hajiya A’ishatu Sani Wali ta bukaci gwamnatocin kasar nan su kara ba fannin kulawa ta musamman cikin kasafin kudin da suke yi a duk shekara.Ta yi wannan tsokaci ne a zantawarta da wakilinmu a karshen wani taro da aka gudanar kan kasafin […]
Shugabar sashen kula da lafiya a matakin farko ta karamar Hukumar Dawakin Tofa, Hajiya A’ishatu Sani Wali ta bukaci gwamnatocin kasar nan su kara ba fannin kulawa ta musamman cikin kasafin kudin da suke yi a duk shekara.
Ta yi wannan tsokaci ne a zantawarta da wakilinmu a karshen wani taro da aka gudanar kan kasafin kudi, inda ta ce fannin lafiya yana bukatar kulawa ta musamman daga rukunin gwamnatoci uku, wato kananan hukumomi da jihohi da kuma tarayya, idan aka dubi muhimmancin bangaren kiwon lafiya ga dan Adam.
Hajiya A’ishatu Sani ta ce idan akwai isassun kudin tafiyar da harkar kula da lafiya, za a wadata asibitoci da magunguna da duk abubuwan da ake bukata dangane da kula da lafiyar al’umma, tare da fatan za a yi la’akari da wannan bukata a dukkan kasafin kudin da ake gabatarwa a matakai uku na gwamnati.
Daga nan sai ta nanata kokarin da sashenta ke yi na daukar ingantattun matakai don ganin an samun nasarar kakkabe cutar shan-inna daga yankin da kuma sauran cututtuka da ke yaduwa musamman ganin yadda karamar Hukumar Dawakin Tofa take bai wa sashen cikakken kulawa a koyaushe.
Sannan ta yi kira ga al’ummar yankin su ci gaba da bayar da goyon baya ga duk wani shiri na gwamnati da ya shafi kula da lafiya ta yadda za a hada hannu wajen kawar da cututtuka da ke zamowa barazana ga rayuwar al’umma. Ta bukaci iyaye mata su ci gaba da kai ’ya’yansu wuraren yin allurar rigakafi da ake gudanarwa lokaci zuwa lokaci a wasu zababbun wurare.