A rika ba kananan mawaka dama – Abba Tiyo

Abba Ahmad wanda aka fi sani da Abba Tiyo matashin mawakin Hip-Hop ne da wakokin nananye a Jihar Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa akwai bukatar manyan mawaka su rika karfafa wa kanann mawaka gwiwa ta hanyar jansu a jiki tare da ba su damar da suke nema wajen yin waka a lokutan […]

A rika ba kananan mawaka dama – Abba Tiyo

Abba Ahmad wanda aka fi sani da Abba Tiyo matashin mawakin Hip-Hop ne da wakokin nananye a Jihar Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa akwai bukatar manyan mawaka su rika karfafa wa kanann mawaka gwiwa ta hanyar jansu a jiki tare da ba su damar da suke nema wajen yin waka a lokutan gudanar da wasanni:

 

Aminiya: Mene ne tarihin rayuwarka a takaice.

Sunana Abba Ahmad Ibrahim Fanshekara wanda aka fi sani da Abba Tiyo.  An haife ni a 1990. Na yi firamare da sakandare duk a Unguwar Fanshekara. Daga nan na tsaya ban ci gaba ba, sai na kama sana’ar dinki na maza da mata.

Aminiya: Yaya aka yi aka yi ka fara harkar waka?

Gaskiya tun ina firamare nake da sha’awar harkar waka amma ban fara ba sai bayan na gama karatun sakandare a shekarar 2017. Tun a wancan lokaci na sha rubuta waka amma ban taba rerawa ko bugawa ba, sai a wannan lokaci na fara. Mafi yawan lokuta ina son wakar Hausa amma wahala take ba ni saboda kari zai zo min amma in rasa yadda zan yi in ci gaba da amfani da shi a sauran baitocin wakar. Musamman idan karin ya zo zan yi baitin namiji amma sai in saka na mace. Allah dai cikin ikonSa daga baya na fara yin Hip-Hop, da yake akwai wani situdiyo a unguwarmu sai na fara zuwa can ana buga min wakata. A shekarar 2018 sai aka shirya wani taron bikin Sallah inda a nan ne na fara yin wakar Hausa.

Aminiya: Zuwa yanzu wakoki nawa ka yi?

A gaskiya wakokina ba su da yawa guda shida ne kacal sai dai akwai wadanda ban buga ba. A shekarar 2017 ce na fara buga wakata ta farko mai taken “Lokaci” wadda mutane da yawa ke min lakabi da ita. Daga baya kuma akwai wasu kamar su Yasim da Zahra.

Aminiya: Shin idan ka yi waka kana bayarwa a duba maka?

Lokacin da na fara waka a unguwarmu babu wani babban mawaki da zan kaiwa ya duba min. To akwai wani wanda ya riga ni fara yin waka da kusan shekara biyar ko shida. To wakata ta farko ma tare muka rubuta ta saboda kamar yadda na fada miki a baya idan na fara yin amshi sai baitin ya gudu, to, amma da na fara aiki da wannan abokin nawa sai aka samu sauki. Idan na kawo wani abu sai ya dora ni har in gama. To har yanzu dai in zan yi waka sai na fara fada masa karin sannan in yi.

Aminiya: Mene ne jigon wakokin naka wani salo suke dauka?

Kusan wakokina na soyayya ne.

Aminiya: Me ya sa ka fi zabar soyayya a jigon wakokinka?

Gaskiya na ga yanzu an fi zabar fannin soyayya ko saye ma za a yi za ki ga an fi sayenta. Kuma a bangaren mutane za ki ga sun fi son wakar soyayya. Kuma yawanci za ki ga sun fi son waka mai kida sosai. Amma ni in son raina ne na fi son wakar da ba kida sosai.

Aminiya: Yaya kake ganin karbuwar Hip-Hop a wannan lokaci?

Gaskiya yanzu  wakokin Hip-Hop sun karu sosai wanda yanzu ma ta fara sabanin shekarun baya. A nan unguwarmu muna da wani da yake hada mana wani taro wanda shi ne ya sa ni na buga waka.

Aminiya: Yaya alakarku take da manyan mawaka da suka shahara?

Gaskiya ba mu da wata alaka mai kyau a tsakaninmu, don za ki ga suna daga wa kananan mawaka irinmu kai. Akwai lokacin da na buga wakata ta farko aka ce za a yi wani taro kuma mu kananan mawaka za mu biya Naira dubu daya, sai na ce to shi ke nan. To akwai wani abokina Jabir tare muka bada kuma muka je. Bayan an fara taron ana ta kiran mawaka amma shiru ba a kira mu ba, sai a ce za a kira mu, za a kira mu, shiru. Sai aka ce bari a sallami baki. Haka dai aka yi aka gama ba a kira mu ba. Gaskiya wannan abu ya bata min rai sosai, amma na ce ba komai. komai lokaci ne wata rana za a kira mu ba tare da mun biya ba kuma mu yi wasa.

Aminiya: Wane hali ake ciki yanzu?

Gaskiya yanzu ba laifi idan kika kwatanta da baya, don yanzu ana dan yi da mu. Ko a makon da jiya mun yi wani taro da muka je da wanda yake koya min waka, sakamakon sun riga ni fara wakar, sai da aka fara sa wakarsu sannan aka sa tawa duk kuwa da cewa sunana a gaban nasu yake. Alhamdulillah mutane sun yaba abin da na yi domin an min liki sosai kuma na ji dadi. Shi ne ma a wurin muka hadu da wani mai suna Tguy, yake cewa yana nemana saboda ya ji wakata a wani taro da muka yi da Sallah. Ya ba ni shawarwari game da sana’ata kuma ya yi min alkawarin cewa zai taimaka min domin in kara samun sahara da daukaka.

Gaskiya za mun ci gaba kwarai domin mu ma muna da gudunmawar da za mu bada wanda nan gaba za a yi alfahari da gudunmawar.

Yaya kake gani da ’yan fim za su rika karbar wakokin?

Gaskiya da za su rika amsa da zai amfane mu. Sun fi daukar sai ka yi suna za su amshi wakarka.  Wannan shi ne kalubalen da muke fuskanta.

Aminiya: Mene ne sakonka ga masoya?

Ina musu fatar alheri Allah Ya bar mu tare. Kuma ina sanar musu cewa kwanan nan za su samu albam dina insha Allah.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50