A rika bin tsarin karba-karba ne a wajen zaben shugabanni ko a bi cancanta?
daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane […]
daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane daban-daban game da batun:
Tsarin karba-karba shi ne ya fi – Muhammadu Manaja
Muhammadu Manaja: “A gaskiya tsarin karba-karba shi yafi musamman ma ga mu ’yan arewa domin ko ba komai dole ne a ramawa kura aniyyarta. Dalili kuwa shi ne kowane dan kasar nan yasan da cewar ’yan kudancin kasar nan sun shafe sama da shekara 14 suna amfana da mulkin karba-karba, to tunda tsarin na kokarin kewayo wa ga yankin arewa ka ga akwai bukatar da muma mu taba. Don haka a ci gaba da tsarin sabodda shi zai fi fa’ida tunda shi yafi daidaita ’yan kasa da suka fito daga yankuna daban-daban ma su al’ummomi mabambanta”