A rika bin tsarin karba-karba ne a wajen zaben shugabanni ko a bi cancanta? 1

daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan  kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane […]

A rika bin tsarin karba-karba ne a wajen zaben shugabanni ko a bi cancanta? 1
A rika bin tsarin karba-karba ne a wajen zaben shugabanni ko a bi cancanta? 1

daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan  kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane daban-daban game da batun:

Tsarin karba-karba ya fi fa’ida  – Alhaji Mele

Alhaji Mele: “A fahimta ta tsarin karba-karbar shi yafi.
Saboda karba-karbar shi ne tsarin da kowane yankin kasar nan za’a iya damawa da shi, sabanin tsarin cancanta. Kodayake mu ’yan arewa mene ne ribar mu a yanzu idan aka ce a dinga bin cancantar dan takara. Ka ga tun da aka kafa wannan dimukradiyyar  a shekrar 1999,  bai wuce shekara uku da muka amfana da shi ba. Kodayake a yanzu ne muke tsammanin tsarin karba-karbar kan iya sa mu samu mulkin.
To ka ga mu a garemu tsarin shi yafi mana alfanu, kuma mu a kullum addu’armu itace, Allah ya kawo mana gwamnatin da za ta samar mana da zaman lafiya musamman mu al’ummomin Arewa-maso-Gabas da muke fama da tashe-tashen hankula.”