A rika bin tsarin karba-karba ne a wajen zaben shugabanni ko a bi cancanta? 2

daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan  kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane […]

A rika bin tsarin karba-karba ne a wajen zaben shugabanni ko a bi cancanta? 2
A rika bin tsarin karba-karba ne a wajen zaben shugabanni ko a bi cancanta? 2

daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan  kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane daban-daban game da batun:

Tsarin karba-karba cutarwa ne  – Dahiru Hassan

dahiru Hassan: ‘’Tsarin karba-karba wani tsari ne da wasu ’yan siyasa suka kawo a kasar nan rana tsaka domin cimma wani buri nasu. Amma idan ana maganar dimukradiyya ne, to barin jama’a ake  su zabi cancanta. Shi tsarin karba-karba da ake amfani da shi a siyasar kasar nan, yana matukar
cutar da al’ummar Najeriya. Domin yana hana jama’a  zaben wanda ya cancanta.
Kuma wata illar  tsarin karba-karba ita ce duk wanda aka
zaba, a tsarin  zai fi mayar da hankali ne ga yankinsa madadin kasa gabaki daya. Don haka a koma bin cancanta maimakon tsarin karba-karba a kasar nan saboda shi ya fi kawo ci gaba.