A rika bin tsarin karba-karba ne a wajen zaben shugabanni ko a bi cancanta? 3
daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane […]
daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane daban-daban game da batun:
Tsarin karba-karba ba dimukradiyya ba ne – Alhaji Iliyasu
Alhaji Iliyasu Muhammad: ‘’ A duka kasashen duniya da ake mulkin dimukradiyya babu kasar da ta yarda da tsarin karba-karba. Ana maganar cancanta ne, wato ana barin jama’a ne su zabi wanda ya cancanta ya shugabance su, ba maganar karba-karba ba. Don haka tsarin
ba dimukradiyya ba ne, tsarin cancanta shi ne dimukradiyya.
Don haka a gaskiya tsarin cancanta shi ne ya kamata a rike a kasar nan ba tsarin karba-karba ba.