A rika bin tsarin karba-karba ne a wajen zaben shugabanni ko a bi cancanta? 4
daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane […]
daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane daban-daban game da batun:
Tsarin karba-karba coge ne – Alhaji Yusha’u
Alhaji Yusha’u Yaro: “Tsarin karba-karba cogen ’yan siyasar zamani ne. Kuma wata dabara ce ta rage tasirin mutanen da ke da rinjaye a siyasan ce. Idan ana maganar dimukradiyya ana batun rinjaye ne, ba yanki ko shiyyar da dan takara ya fito ba. Don haka tsarin cancanta shi ne kadai tsarin dimukradiyya.”