A rika bin tsarin karba-karba ne a wajen zaben shugabanni ko a bi cancanta? 5
daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane […]
daya da cikin hanyoyin da jam’iyyun siyasar kasar nan kan bi wajen tsayar da ’yan takara shi ne tsarin karba-karba, wanda wasu suke ganin hakan ya sa ba a ba da muhimmancin da yakamata ga cancantar dan takara. Shin ko ya dace a rika bin tsarin karba-karba ko kuma cancanta wajen zabe? Ga ra’ayoyin mutane daban-daban game da batun:
Tsarin cancanta shi ne ya fi – Hamza Magaji
Hamza Magaji: “A siyasance a duk fadin duniya, inda duk ake gudanar da mulkin dimukradiyya, ana zaben shugabanni ne ta hanyar cancantar ’yan takara. Ba tare da la’akari da wace kabila, ko addini ko kuma yankin da suka fito ba. Saboda idan ana maganar ci gaban kasa, to ko daga wane yanki mutum ya fito ya dace ya yi wa kasa baki daya ne aiki. Ba wai shiyyar da ya fito ba. Idan da wannan tsarin muke bi, ka ga da an samu ci gaba a kasa baki daya.”