A rika daurin rai-da-rai ga masu fyade – Darakta
Babbar Daraktar Hukumar Kare Hakkin Yara da Mata, Barista Mariam Haruna Kolo ta bukaci a rika zartar da hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin aikata fyade ta kowace fuska.Barista Mariam Haruna Kolo ta bukaci haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinta da ke Minna kan yadda […]
Babbar Daraktar Hukumar Kare Hakkin Yara da Mata, Barista Mariam Haruna Kolo ta bukaci a rika zartar da hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin aikata fyade ta kowace fuska.
Barista Mariam Haruna Kolo ta bukaci haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinta da ke Minna kan yadda al’amarin fyade ya zama ruwan dare a sassan kasar nan a ’yan shekarun nan.
Daraktar ta ce hukumarta za ta dauki duk matakan da suka dace domin hukunta wadanda aka tabbatar da aikata wannan mummunan laifin da ta ce na marasa cikakken hankali da sanin ya kamata.
Ta kara da cewa, “hukumata ta bullo da shirye-shiryen masu dama da muke sa ran gudanarwa ba tare da bata lokaci ba, domin mu samu nasarar inganta rayuwar mata da yara da suke bukatar taimako, wadanda kididdiga ta nuna cewa sun fi fadawa cikin mawuyacin halin rayuwa a yanzu.
Daraktar ta nuna takaici kan yadda ake samun karuwar mutanen da ke dora wa ’ya’yansu kanana tallace-tallace musamman a nan Arewa, inda ta ce wannan ba karamar barazana ba ce ga rayuwar yaran da ya kamata a ce an samar musu da ilimin addini da na zamani. “Ina yi kira ga iyaye maza su bayar da gudunmuwa wajen kula da tarbiyyar ’ya’yansu domin rage yawan yara masu talla. Wadannan yara amana ce Allah Ya ba su, dole ne su kula da su yadda ya kamata ta yadda za su ci moriyarsu a zaman duniya, sannan gobe kiyama su samu babban rabo a wurin Allah.