A rika fassara zaman da ’yan majalisa ke yi da harsunan Najeriya – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga mmajalisun dokoki da gwamnatoci su rika fassara zaman da ’yan Majalisar Dokoki ta kasa da takwarorinta majalisun dokoki na jihohi suke yi da harsunan Hausa da Yarbanci da Ibo da sauran manyan harsunan […]

A rika fassara zaman da ’yan majalisa ke yi da harsunan Najeriya – Sheikh Jingir
A rika fassara zaman da ’yan majalisa ke yi da harsunan Najeriya – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga mmajalisun dokoki da gwamnatoci su rika fassara zaman da ’yan Majalisar Dokoki ta kasa da takwarorinta majalisun dokoki na jihohi suke yi da harsunan Hausa da Yarbanci da Ibo da sauran manyan harsunan Najeriya, domin ’yan Najeriya su rika fahimtar abubuwan da wakilansu suke yi a majalisun.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a wajen rufe gasar karatun Alkur’ani Mai girma ta kasa na kungiyar, karo na 20 da aka gudanar a garin Jos.
Sheikh Jingir ya ce “Muna kira ga gwamnatin Najeriya ta sanya na’urorin fassara harsunan kasar nan, a majalisun tarayya da na jihohi, domin a rika fassara abubuwan da ’yan majalisar suke yi da harsunan Hausa da Yarbanci da Ibo. Domin ’yan Najeriya su rika fahimtar abubuwan da wakilansu suke yi a zaman majalisun. Bai kamata a rika amfani da harshen Ingilishi da ’yan mulkin mallaka suka bar mana ba, a zauran majalisun kasar nan wadanda mafiya yawan ’yan Najeriya ba sa fahimtarsa. Domin wadannan ’yan majalisa suna wakiltar ’yan Najeriya ne ba Turawan Ingila ba. Domin haka ina kira ga al’ummar Najeriya su fito su yi magana kan wannan al’ammari na fassara zaman da ’yan majalisar suke yi, domin a rika fahimtar abubuwan da suke gudana a majalisun.”
Sheikh Jingir ya roki fadar Shugaban kasa da Majalisar Tarayya kan a dawo da rubutun ajami a jikin takardun kudin kasar nan. Ya ce “Domin muna da tarihin rubutun ajami a kasar nan, tun kafin zuwan Turawa don haka bai kamata a cire rubutun ajami a jikin kudin kasar nan ba.”
Ya yi kira ga Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar kan ya yi magana a kan wannan al’amari, domin a dawo da rubutun ajami a kudin kasar nan.
Ya yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda yake ta kokarin ganin al’ummar Najeriya sun koma kan harkokin noma gadan-gadan. Ya ce babu shakka Shugaban kasa ya nuna wa jama’a soyayya da ya tsaya wajen ganin sun koma ga noma.
Ya ce tsadar abinci da ake fama da ita a kasar nan da zarar amfanin gonar da aka shuka ya nuna za ta sauka domin an yi shekaru da dama rabon da a yi noma irin na bana.