A rika kawo dauki ga marayu da matan da suka rasa mazajensu – Hajiya Gambo Aji
Jihar Yobe jiha ce da yawan yara marayu da matan suka rasa mazajensu sanadiyar cutar kanjamau da rikicin Boko Haram ke karuwa, kan haka ne Aminiya ta tattauna da Shugaba (Amira) ta kungiyar ’Yan uwa Mata Musulmi ta kasa (MSO) reshen jihar, Hajiya Gambo Aji Suleiman kan lamarin da kuma da kuma yadda suke gudanar […]
Jihar Yobe jiha ce da yawan yara marayu da matan suka rasa mazajensu sanadiyar cutar kanjamau da rikicin Boko Haram ke karuwa, kan haka ne Aminiya ta tattauna da Shugaba (Amira) ta kungiyar ’Yan uwa Mata Musulmi ta kasa (MSO) reshen jihar, Hajiya Gambo Aji Suleiman kan lamarin da kuma da kuma yadda suke gudanar da ayyukansu:
Aminiya: Mene ne muhimman kudirorin wannan kungiya taku kuma a nan Jihar Yobe ne take gudanar da ayyukanta ko a kasa baki daya?
Hajiya Gambo Aji: To a gaskiya wannan kungiya tamu tana gudanar da ayyukanta ne a kasa baki daya kuma muna da hedikwatarmu ce a garin Kano, kuma a yanzu haka muna da rassa a kimanin jihohi 18 da ke Arewa. Muhimman kudirorinmu sun hada da tallafa wa mata gajiyayyu da wadanda suka rasa mazajensu da marayu kai har da matan aure da suka hadu da wasu matsaloli na rayuwa, a bangaren abinci ko sutura ko makaranta ko kiwon lafiya, duk mukan taimaka musu gwargawado.
Aminiya: To ina kuma ga matan da suke dauke da cutar ta kanjamau su kai-tsaye kukan taimaka musu?
Hajiya Gambo Aji: kwarai da gaske mukan taimaka wa mutanen da ke dauke da cutar kanjamau, matukar mutum ya kawo kansa gare mu musamman da yake ina daya daga cikin jami’an Hukumar Yaki da Cutar kanjamau ta Jihar Yobe (YOSACA), ka ga ashe an yi yanka ne a kan gaba.
Aminiya: Shin wannan kungiya taku daga ina take samun tallafin da kuke iya gudanar da ayyukanku?
Hajiya Gambo Aji: Alal hakika mukan samu tallafi ne daga wurare daban-daban da suka hada da gwamnatin Jihar Yobe da wasu kungiyoyi na cikin gida Najeriya da Majalisar dinki Duniya musamman da yake muna da hadin gwiwa da Hukumar YOSACA da ke kula da masu cutar kanjamau sai kuma daidaikun mutane da sauransu.
Aminiya: Da yake kukan tallafa wa matan da suka rasa mazajensu da marayu da masu cutar kanjamau, gajiyayyu da ba su da cin yau bare na gobe, yaya kuke iya kaiwa gare su?
Hajiya Gambo Aji: To yadda lamarin yake shi ne a yanzu haka mun kai kusan shekara goma muna dawainiya a wannan kungiya, to ba mu muke neman mutanen ba, a’a da kansu suke zuwa wurinmu. Alal misali idan muka kai tallafi ga wata mace ta yiwu ta fada wa wata mai matsala irin tata, to ta haka masu matsaloli ke zuwa wurinmu. Yanzu akalla muna da jerin yara marayu sama da 200 da muke tallafa mawa da kuma mata da ke da yawa da su ma muke agaza musu da dan abin da muke samu daga kayayyakin tallafi.
Aminiya: Idan mabukatan suka zo da bukatunsu, ko daga baya kukan bi su zuwa gidajensu ne don tabbatar da halin da suke ciki?
Hajiya Gambo Aji: Lallai wannan aiki muna yin sa kwarai da gaske saboda sanin a halin da ake ciki mayaudara sun yi yawa domin wadanda suke da hali ma kan zo su yi mana karyar ba su da shi, don haka muna da mambobinmu da suke bin gidajen duk wadanda suke zuwa da bukatarsu, in an gano gaskiya ne, sai mu je Ma’aikatar Kula da Addini mu karbi mota don zuwa duba halin da suke ciki a gidan suke domin duba wane irin tallafi suke bukata.
Aminiya: Ganin cewa kuna tallafa wa masu cutar kanjamau, wane kira kuke da shi ga masu boye cutar maimakon su fito neman magani?
Hajiya Gambo Aji: To a gaskiya dama mukan fadakar da wasu daga cikin masu cutar kanjamau cewa su rika sanar da ’yan uwansu da ke dauke da cutar da suke boye kansu kan irin taimakon da suke samu daga wannan kungiya da kuma gwamnati game da abin da ya shafi maganin cutar da kayayyaki don su ma su amfana maimakon boye kansu. Don haka ina kira ga mutanen da suke dauke da cutar kanjamau amma suke boye kansu kan su rika fitowa don bayyana kansu, saboda in suka boye cuta sai cutar ta yi musu illa.