‘A rika koyar da rubutun Ajami a makarantun kasar nan’

Wani malamin addinin Musulunci da ke garin Jos a Jihar Filato Malam Abdurrahaman Ahmad Husaini ya bukaci Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanya koyar da rubutun Ajami a manhajar koyarwa ta makarantun kasar nan. Malam Abdurrahaman Husaini ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce yin haka […]

‘A rika koyar da rubutun Ajami a makarantun kasar nan’
‘A rika koyar da rubutun Ajami a makarantun kasar nan’

Wani malamin addinin Musulunci da ke garin Jos a Jihar Filato Malam Abdurrahaman Ahmad Husaini ya bukaci Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanya koyar da rubutun Ajami a manhajar koyarwa ta makarantun kasar nan.

Malam Abdurrahaman Husaini ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce yin haka ba karamin tasiri zai yi ba wajen bunkasa ilimi a kasar nan.
Ya ce a tarihin Najeriya tun kafin Turawan mulkin mallaka su shigo, ana amfani da rubutun Ajami, kuma har lokacin da aka samu ’yancin kai an ci gaba da yin amfani da rubutun Ajami wajen rubuce-rubucen abubuwan da suka shafi al’amuran yau da kullum musamman a Arewacin Najeriya.
Ya ce rubutun Ajami yana da tasiri wajen gudanar da harkokin ilimi, inda ake da mutane da dama da suke amfani da shi a Arewa.
Malam Abdurrahaman ya nuna takaici kan yadda Babban Bankin Najeriya yake cire rubutun Ajami a takardun kudin kasar nan. Ya ce rubutun Ajami ilimi ne ba alama ce ta wani addini ba. Don haka abin da Babban Bankin Najeriya ya yi bai dace ba.
Kuma ya bukaci Babban Bankin ya sake duba wannan mataki da ya dauka ya dawo da rubutun Ajami a jikin kudin.
Ya yi kira ga masu hanu da shuni na Arewa su fito su bude jaridu da mujallun Ajami don bunkasa wannan rubutun.

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista