‘A rika kyautata wa tsofaffin sojoji’

Shugaban Kungiyar ’Yan Fansho ta Jihar Sakkwato Alhaji Umaru Abubakar Mazara Tambuwal ya ce bai kamata a rika mantawa da ’yan mazan jiya ba, wajen biyansu hakkokinsu. Ya ce “Bikin da ake yi shekara-shekara a kasar nan abu ne mai kyau domin a kara sanar da mutane irin gudunmawar da tsofaffin sojoji suka bayar na […]

‘A rika kyautata wa tsofaffin sojoji’

Shugaban Kungiyar ’Yan Fansho ta Jihar Sakkwato Alhaji Umaru Abubakar Mazara Tambuwal ya ce bai kamata a rika mantawa da ’yan mazan jiya ba, wajen biyansu hakkokinsu.

Ya ce “Bikin da ake yi shekara-shekara a kasar nan abu ne mai kyau domin a kara sanar da mutane irin gudunmawar da tsofaffin sojoji suka bayar na gina kasar nan da dunkule ta wuri daya, abu ne da za a rika jinjina musu kan sadukarwa ba a jefar da ita ba.”

Ya bayyana haka ne a wurin bikin ’yan mazan jiya da aka yi a Sakkwato. Ya ce bayan bikin da ake yi na karrama ’yan mazan jiya akwai bukatar gwamnati ta duba tsarin kudin fansho da ake ba su, inda ya ce wasu jihohin tsofaffin sojoji na shan wahala, fanshon da suke karba bai taka kara ya karya ba.

Ya ce akwai bukatar jihohin Najeriya su yi koyi da Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal wurin biyan fansho a kan kari. Ya ce kafin zuwan gwamnatinsa masu karbar fansho a jihar sun koma tamkar almajirai, ba su san ranar biyansu ba, sabanin yanzu da ake biyan albashi tare da fansho.

Ya ce suna kallon Gwamnan a matsayin Gwamnan ’Yan fansho “Domin gwargwadon iyawarsa ya yi wa masu karbar fansho a Sakkwato riga da wando, sai dai su yi ta yi masa addu’a,” inji shi.

Mazara ya ce yana mamakin wasu jihohi da gwamnoninsu suka mayar da biyan fansho kamar kyauta suke yi wa masu karba ba hakkinsu ba ne, inda ake kwashe sama da wata biyar ko hudu ba a biya fansho a wata jihar ba.

“Mutane da lokacin ajiye aikinsu ya zo, sai hankalinsu ya tashi su shiga rudu da neman makama domin sun san da sun bar aiki, kudin da ke zo musu a wata sun yanke. Kan haka sai ka samu ana ta gyaran fayil kada dai a tafi, sabanin nan Sakkwato da har mutum so yake yi lokacin ritayarsa ya yi ya je ya huta,” inji Tambuwal.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta