‘A rika taka-tsatsan wajen amfani da kayayyakin lantarki’

Shugaban Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Shiyyar Yola da ke kula Damaturu Alhaji Usman Abubakar Wakta ya bukaci masu amfani da wutar lantarki su rika amfanin da kayayyakin wutar lantarki ta hanyoyin da suka dace don kauce wa shiga mummunan yanayi.Shugaban ya yi kiran ne yayin ganawarsa da Aminiya kan yadda ake samun yawaitar katsewar wutar […]

‘A rika taka-tsatsan wajen amfani da kayayyakin lantarki’
‘A rika taka-tsatsan wajen amfani da kayayyakin lantarki’

Shugaban Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Shiyyar Yola da ke kula Damaturu Alhaji Usman Abubakar Wakta ya bukaci masu amfani da wutar lantarki su rika amfanin da kayayyakin wutar lantarki ta hanyoyin da suka dace don kauce wa shiga mummunan yanayi.
Shugaban ya yi kiran ne yayin ganawarsa da Aminiya kan yadda ake samun yawaitar katsewar wutar lantarki a garin Damaturu fadar Jihar Yobe.
Alhaji Usman Abubakar ya ce, a mafi yawan lokaci yin sakaci ta wajen barin kayayyakin da ke amfani da wutar lantarki a kunne bayan dauke wutar lantarki  ke haddasa gobara da zarar an sake dawo da wutar lantarkin.
Alhaji Usman Abubakar ya ci gaba da cewa akwai bukatar jama’a su rika amfani da kayayyakin lantarki masu inganci musamman wayoyi yayin da suka zo jan wutar lantarki a gidaje ko ofisoshi da wuraren kasuwancinsu. Ya ce kasancewar jihar tana cikin sassan da suke fama da zafi duk wata wayar da ba ta da inganci takan iya narkewa cikin sauki.
Shugaban ya ce a mafi yawan lokaci akan tarar da jama’a na kokarin gina gidaje da wuraren kasuwanci na milyoyin Naira amma kuma sai a tarar suna amfani da kayayyaki marasa inganci wajen sanya wutar lantarki a wuraren.
Ya ce yawan dauke wutar lantarki na faruwa ne sakamakon matsalolin da kamfanin rarraba wutar lantarkin na kasa ke fuskanta kuma masu ruwa da tsaki kan lamarin na kokari domin shawo kan lamarin nan da karamin lokaci.