A rika tunawa da wadanda suka taimaka wa Malam Aminu Kano – Binta Sarki Mukhtar

Shugabar gidan rediyon Rahama da ke Kano, Hajiya Binta Sarki Kukhtar ta bukaci a rika tunawa da mutanen da suka taimaka wa Malam Aminu Kano lokacin gwagwarmyarsa ta kwato ’yancin talaka.Hajiya Binta Mukhtar ta bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a wajen bikin tunawa da Marigayi Malam Aminu Kano da Cibiyar Bincike […]

A rika tunawa da wadanda suka taimaka wa Malam Aminu Kano – Binta Sarki Mukhtar
A rika tunawa da wadanda suka taimaka wa Malam Aminu Kano – Binta Sarki Mukhtar

Shugabar gidan rediyon Rahama da ke Kano, Hajiya Binta Sarki Kukhtar ta bukaci a rika tunawa da mutanen da suka taimaka wa Malam Aminu Kano lokacin gwagwarmyarsa ta kwato ’yancin talaka.
Hajiya Binta Mukhtar ta bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a wajen bikin tunawa da Marigayi Malam Aminu Kano da Cibiyar Bincike kan Al’amuran Siyasa da Horarwa da ke Gidan Mambayya ta shirya karo na 33.
Haijya Binta ta ce bai kamata tarihi ya mance da mutanen da suka tallafa wa Malam Aminu Kano wajen gwagwarmayar tabbatar da ’yancin talaka da suka yi amfani da jiki da dukiyarsu ba.
“Kamar yadda ake cewa bishiya daya ba ta samar da daji, Malam Aminu Kano ya yi gwagwarmayar tabbatar da talaka ya samu ’yanci a kasar nan, kuma hakan bai samu ba sai da taimakon wadansu mutane. Akwai mutane ’yan NEPU da suka taimaka wa Malam Aminu wadanda su ne manyan sahabbansa wajen fafutikar da ya yi a tsawon rayuwarsa. Ita kanta Jam’iyyar NEPU mutum takwas ne suka kafa ta. Don haka akwai bukatar duk lokacin da aka tashi shirya irin wannan lacca ya kamata a rika hadawa da wadancan mutane. Hakan zai sa wadanda ba su san abin da ya faru a wancan lokaci ba, su san tarihi. Kuma hakan zai taimaka sauran jama’a musamamn ’yan siyasa su yi koyi da irin rayuwar da suka gudanar,” inji ta.
A jawabin Hajiya Na’ja’atu Muhammad ta yi kira ne ga ’yan siyasa su yi koyi da rayuwar Malam Aminu ba kawai su rika fadin tarihiinsa a baki ba. “Mu NEPU ce ta haife mu mun tashi mun ji yadda tarihi ya nuna yadda iyayenmu suka sha wuya a fannin gwagwamaryar siyasa. A yanzu ’yan siyarsar wannan zamani suna so su sha irin waccan wahalar da iyayenmu suka sha? Amsar ita ce a’a ’yan siyasarmu na yanzu kudi da mukami kawai suke so. Akwai jan aiki a gabanmu matukar muna so mu yi koyi da rayuwar gwagwarmaya irin ta su Malam Aminu Kano,” inji ta.
Mutane da dama ne suka gabatar da makaloli a wajen bikin da suka hada da fitaccen malamin tarihin nan na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, Farfesa Sule Bello da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da sauransu.