A rika yawaita tuba da istigfari ga Allah
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificn halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa. Bayan haka, a kowane lokaci ana son Musulmi ya rika tuba ta hanyar furuci da kokarin barin aikata zunubai tare da aikata kyawawan ayyuka, saboda bai san yaushe ajalinsa zai zo ba. […]
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificn halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.
Bayan haka, a kowane lokaci ana son Musulmi ya rika tuba ta hanyar furuci da kokarin barin aikata zunubai tare da aikata kyawawan ayyuka, saboda bai san yaushe ajalinsa zai zo ba. Tuba ga Allah abu ne wajibi kuma abu ne mai sauki. Wato a nemi gafarar Allah da harshe da zuciya kamar yadda Allah Madaukaki Ya nuna: “Kuma wanda ya aikata cuta ko kuwa ya zalunci kansa, sannan ya nemi Allah gafara, zai samu Allah Mai gafara ne, Mai jin kai.” (k:4:110).
Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Na rantse da Wanda raina yake hannunSa, da za a ce ba ku yin kuskure, sai Allah Ya shafe ku duka, Ya kawo wadansu mutane da za su yi kuskure su roki Allah gafara don Ya gafarta musu.” Muslim ya ruwaito.
Ga wasu ayoyi da suke magana kan istigfari da tuba ga Allah, kuma da irin yadda magabata suke daukar zunubi da ka’idojin karbar tuba da yadda ya kamata a yi addu’a.
1. Istigfari dabi’a ce ta mutanen da Allah zai ba su nasara ko babban rabo:
Allah Madaukaki Ya ce: “(Sai ’yan wuta suka ce), Ya Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sannan idan mun koma (ga aikata barna), to, lallai ne, mu ne masu zalunci.” Ya ce, “Ku tafi (da wulakanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana. Lallai wasu kungiyoyi daga bayiNa sun kasance suna cewa, “Ya Ubangijinmu! Mun yi imani, sai Ka gafarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alherin masu tausayi. Sai kuka rike su leburori (wulakantattu).” (k:23:107-110). Shi ke nan magana ta kare? A’a sai Allah Ya ce: “Lallai ne, Ni Ina saka musu a yau, saboda abin da suka yi wa hakuri. Domin lallai ne, su, su ne masu samun babban rabo.” (k:23:111).
2. Istigfari na bude kofofin alheri a duniya da Lahira.
A lokacin Halifancin Amirul Mumina Umar bin Khaddabi (RA) an samu kamfan ruwa a Madina, bayan an yi shelar sallar rokon ruwa, sai Umar (RA) ya hau mumbari a cikin hudubarsa ya fi karanto ayoyin da suka yi magana kan istigfari. A wancan rana ya karanto abin da Annabi Nuhu (AS) ya fada ga mutanensa: “Na ce, “Ku nemi gafara daga Ubangijinku, lallai ne Shi Ya kasance Mai gafara ne. Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai bubbuga. Kuma Ya yalwata muku game da dukiya da ’ya’ya, Ya sanya muku (albarka) ga gonaki, kuma Ya sanya muku koguna.” (k:71:10-12).
3. Istigfari na nuna mutanen da suka fi soyuwa a wurin Allah:
Abu Huraira (RA) ya ce: “Ya ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Na rantse da Allah, Ni ina rokon Allah gafara da tuba a gare Shi a wuni fiye da sau saba’in.” Sannan ga labarin Annabi Ayyuba (AS) cewa: “(Muka ce), Kuma ka riki wani kulli da hannunka, ka yi duka da shi, kuma kada ka karya rantsuwarka. Lallai ne Mu, Mun same shi mai hakuri. Madalla da bawa, shi. Lallai shi mai mayar da al’amari (tuba) ga Allah ne.” (k:38:44).
4. Ganin girma da munin zunubi:
Hadisin Ma’iz yana nuna yadda ake istigfari da yadda gaskiyar tuba ga Allah take. Abin da ya faru Ma’iz shi ne ya yi zina, kuma ya zo ga Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya Manzon Allah! Na yi zina!” Sai Manzon Allah ya kawar da kai daga gare shi, ta yadda Ma’iz zai hakura ya tserar da kansa daga haddi, amma sai Ma’iz ya ci gaba da komawa ta gaban fuskar Annabi (SAW) yana maimaita “Na yi zina! Na yi zina!!”
Da Ma’iz ya yi ta nanata haka sai Manzon Allah (SAW) ya tambaye shi: “Shin kai mahaukaci ne?” Ya ce: “A’a.” “Shin ka sha giya ne (ya nemi wani ya sunsuna bakinsa)?” Ya ce, “A’a.” Ya ce: “Kuma ka shige ta?” Ya ce: “Eh!”
Sai Manzon Allah (SAW) ya tambaye shi a hankali, “To wai me kake so da kake bayyana wannan abu?” Sai Ma’iz ya ce: “Ina so ne ka tsarkake ni!”
Irin wannan karfin imani da ya sa Ma’iz irin wannan tuba ga Allah da za a raba shi da ya ishi dukan mutane Madina, kamar yadda karshen Hadisin ya nuna.
Sannan Hilal bin Sa’ad ya ce: “Kada ka dubi kankantar zunubinka, ka dubi girman Wanda kake saba maSa (Allah)!”
5. ka’idojin tuba ta gaskiya:
Anas (RA) ya ruwaito Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Dukan ’yan Adam masu kuskure ne. Amma mafiya alherin masu kuskure su ne masu tuba.” Tirmizi ya ruwaito. Imam Nawawi (RH) ya rubuta cewa ana neman gafara kan kowane zunubi. Idan wannan zunubi tsakanin bawa da Ubangiji ne, bai shafi hakkin wani ba, to akwai ka’ida uku na karbar wannan tuba:
1. Daina aikata wannan zunubi.
2. Yin nadama kan abin da ya gabata.
3. Da niyyar ba za a koma ga aikata zunubin ba. Idan aka rasa daya daga cikin wadannan ka’idoji to akwai nakasu ga wannan tuba.
Idan kuma akwai hakkin wani to sharadi na hudu zai shigo. Wato mutum ya mayar wa mai hakki, hakkinsa. Misali idan ya saci kayansa ne ya mayar masa, idan ya mare shi ya ba shi dama ya rama, ko ya nemi ya yafe masa, idan ya zage shi ne ya nemi ya yafe masa.
Ga wata kissa nan don nazari:
Wata rana bayan an tafka ruwan sama Hisham bin Hasan yana tafiya a bayan Al’ala bin Ziyad a wata hanya mai tabo a kauyensu. Sai ya lura Ziyad yana kauce wa ruwan da ke gudu a gefen hanya tare da tabo, sai wani ya tunkude shi har takalminsa ya zame ya ja shi cikin ruwan. karfin igiyar ruwan ya tilasta Ibnu Ziyad ya koma daya gefen.
Bayan sun isa gida sai Ibnu Ziyad ya juyo ga Hisham ya ce: “Yadda muke kauce wa tabo da igiyar ruwa a kan hanyarmu ta zuwa gida, haka ya kamata Musulmi ya kauce wa saba wa Allah a daukacin tafiyar da yake yi zuwa Lahira. Kuma kamar yadda ka ga igiyar ruwa ta ja ni, haka igiyar zunubi take jan mutum lokacin da ya fada cikinta, za ta yi ta jan sa tana dulmiyar da shi yana dada nutsewa.”
Mu dauki misalin abin da ya faru da Bani Isra’ila lokacin Annabi Musa (AS), lokacin da Fir’auna ya dauki matakin karshe na gamawa da su. Annabi Musa (AS) ya jagoranci tsofaffi maza da mata da yara na Bani Isra’ila don gudun darkakewar Fir’auna, suka nufi bakin teku, ba su da jirgin ruwa, ba su da ko da kwale-kwale da za su hau domin su gudu. Ga Fir’auna ya taso su a gaba, ba su da makamin da za su iya juyawa su fuskanci rundunar Fir’auna. Sun isa bakin teku ruwa iya kallonsu, sun waiwayawa baya, ga Fir’auna cike da fushi, mayakansa rike da miyagun makamai, sukwane kan dawaki sun nufo su. Sai suka koka ga Annabi Musa (AS) kamar yadda Alkur’ani Mai girma ya ba mu labari: “Sa’an nan lokacin da jama’a biyu suka ga juna, sai sahabban Musa suka ce: “Lallai ne mu, hakika, wadanda ake riska ne.” (k:26:61).
Annabi Musa (AS) ya ba su, amsar da take nuna karfin imani: “Ya ce “Kayya! Lallai ne Ubangijina Yana tare da ni, zai shiryar da ni (hanyar tsira).” (k:26:62). Sai Allah Ya ce: “Sai Muka yi wahayi zuwa ga Musa cewa: “Ka doki teku da sandarka.” Sai teku ta tsage, kowane tsagi ya kasance kamar falalen dutse mai girma. Kuma Muka kusantar da wadansu mutane (su Fir’auna) a can. Kuma Muka tserar da Musa da wadanda suke tare da shi gaba daya. Sannan Muka nutsar da wadancan (su Fir’auna).” (k:26: 63-66).
A lokacin da Fir’auna ya ga kansa a tsakiyar teku ya tabbata mutuwa ta zo masa ne, sai ya ce: “Na yi imani cewa, hakika, babu abin bautawa face wannan da Banu Isra’ila suka yi imani da Shi. Kuma ni ina daga Musulmi.” (k:10:90).
Ibnu Abbas ya ce a ranar da Fir’auna ya fada cikin teku ya fahimci zai mutu, sai Mala’ika Jibril ya zo masa ya rika rika watsa wa fuskarsa tabo yana cika masa baki da shi, don kada ya samu damar rokon rahamar Allah, wanda da ya roka da an ba shi. Allah Ya fada wa Fir’auna da sauran mutanen da ba su tuba, sai sun ga mutuwa cewa: “Ashe a yanzu (ne za ka tuba ka yi imani)! Alhali kuwa hakika ka saba a gabani, kuma ka kasance daga masu barna?” (k:10:91).